‘Yar Arewa Farfesa mafi ƙarancin shekaru a Najeriya

    0
    752

    A garin Zariya na jihar Kaduna aka haifi Aisha Sani Maikudi ‘yar asalin jihar Katsna a Najeriya, a ranar 31 ga Janairu, 1983. Ta yi jarabawar kammala sakandare ta WASSCE a makarantar Queens College a Legas, ta kuma yi digirin ta na farko a fannin shari’a wato LLB a Jami’ar Reading a ƙasar Ingila, ta kuma yi karatu digiri na biyu (LLM) a makarantar tattalin arziki ta Landan, sannan tayi makarantar lauyoyi wato shoool of law a Abuja a Najeriya sannan tayi digirin digirgir wato PhD a jami’ar Abuja.

    A shekarar 2007, Aisha ta yi hidimar ta ƙasa a sakatariyar kamfanoni da sashin shari’a na kamfanin man fetur na Najeriya, a shekarar 2008 ta shiga Jami’ar Abuja a matsayin Malama mai mataki na 2, sannan ta zama mace ta farko kuma ƙaramar shugabar sashen koyarwar shari’a a shekarar 2014; mace ta farko kuma ƙaramar mataimakiyar shugaban jami’ar Abuja, a tsangayar karatun shari’a a shekarar 2018 kuma ta zama darakta na farko a Jami’ar Abuja.

    KU KUMA KARANTA:Musulma ‘yar Arewa ta kafa tarihin zama mace ta farko a matsayin lauyan manyan kotunan Ingila da Wales

    Har ila yau ita ce Farfesa mafi ƙarancin shekaru a jami’ar Abuja da ma Najeriya, sannan kuma ita ce Farfesa mace ta farko a fannin shari’a a yankin Arewa maso Yamma da kuma Jami’ar Abuja.

    Ta kware a dokar majalisar ɗinkin duniya, kuma ta yi rubuce-rubuce da yawa a kan yankin. A’isha ta yi shawagi da kwasakwasai na digiri na biyu a kan Dokar Majalisar ɗinkin Duniya kuma ta ƙula da ayyuka masu yawa na digiri da na gaba.

    Ta kuma koyar da dokar kamfani fiye da shekaru 12 kuma ta ƙware a kan injina.

    Aisha ta halarci taruka da horo da dama a duniya, kuma mamba ce a ƙungiyoyin ƙwararru daban-daban da suka haɗar da; ƙungiyar lauyoyin Najeriya, ƙungiyar malaman shari’a ta Najeriya da ƙungiyar lauyoyin mata ta duniya. Aisha tana da aure da ‘ya’ya.

    Leave a Reply