Musulma ‘yar Arewa ta kafa tarihin zama mace ta farko a matsayin lauyan manyan kotunan Ingila da Wales

3
309

Wata ‘yar Najeriya mai suna Munayah Yusuf Hassan ta kafa tarihi a matsayin mace ta farko daga yankin arewacin Najeriya da aka shigar da ita a matsayin lauyar manyan kotunan Ingila da Wales.

Audu Bulama Bukarti, babban manazarci a cibiyar Tony Blair ne ya sanar da hakan a shafinsa na Facebook a ranar Asabar, 3 ga Satumba, 2022.

A cewar Bulama, Mrs Hassan ita ce mace ta farko ‘yar asalin Arewa da ta samu wannan nasara. Bulama ya ƙara da cewa, Uwargidan Yusuf ta kammala karatun digiri a fannin shari’a na Jami’ar Bayero ta Kano, kuma an kira ta zuwa makarantar ƙwarewar aikin lawyer ta Najeriya, kafin ta koma Ingila tare da mijinta.

Ya kuma bayyana lauyar a matsayin mai tawali’u da aiki tukuru.

“Ga Munayah Yusuf Hassan, mace ta farko a Arewacin Najeriya da aka shigar da ita a matsayin Lauya ta Manyan Kotunan Ingila da Wales (a sanina).

A jiya ne aka gudanar da bikin shigar ta a Landan. Munayah an haifeta kuma ta girma a Kano kuma ta kammala karatunta a Jami’ar Bayero kafin ta wuce Makarantar Shari’a ta Najeriya kuma aka kira ta zuwa makarantar ƙwarewar aikin lawyer ta Najeriya.

Ta koma kasar Ingila ne bayan ta auri mijinta, mai ƙwarewa a fannin zanen gine-gine, ɗan Najeriya da ke zaune a can. Munayah fitila ce ta aiki tuƙuru, juriya, tawali’u, kyautatawa da ƙwazo. Da fatan wannan ya zama albarka ga Munayah, danginta, abokai da sauran al’umma.

Ina fatan wannan ze zaburar da mu duka don yin aiki tuƙuru don cimma burinmu.” Bulama ya buga.
.

3 COMMENTS

Leave a Reply