Na fara sana’a ne don na dogara da kaina – Zainab Aqeela Katsina

0
255

Daga Ibraheem El-Tafseer

Zainab Aqeela Katsina, matashiya mai sana’ar Dambun naman Kaji. Ta shahara sosai a kafofin sada zumunta, wajen tallata sana’arta ta Dambun naman Kaji, kuma tana samun ɗimbim masu saye a wannan kafa ta social media ɗin, a garuruwa daban-daban. Neptune Hausa ta zanta da ita kan wannan sana’a da kuma yadda aka yi ta fara. Hirar ta tavo abubuwa da dama, ga yadda hirar ta kasance;

NEPTUNE HAUSA: Ki gabatar da kanki ga masu karatunmu.

ZAINAB AQEELA: Sunana Zainab Lawal Abdulƙadeer. Ni haifaffiyar Katsina ce. A nan na yi Firamare da Sakandire, yanzu ga shi ina Diploma.

NEPTUNE HAUSA: Ko meye ya ja ra’ayinki kika fara yin sana’a, ganin cewa mafi yawan ‘yan mata suna ɗora nauyin komai nasu ne a iyayensu?

ZAINAB AQEELA: Dalilin da ya sa na fara sana’a shi ne domin na dogara da kaina. Ganin cewa abubuwa sun yiwa iyaye yawa, wani abin ma suna so su yi maka, amma saboda ga ƙannenka, ga kuma wasu yayyenka, waɗanda su ma ba su wuce a yi musu ba. To sai ka ga abubuwan sun yi yawa, ba za ku samu abin da kuke so yadda ya kamata ba. To amma idan kana sana’a, sai ka ga ma kana taimaka wa iyayen da wasu abubuwan. Babban abin da ya sa na fara sana’a, shi ne don na dogara da kaina.

NEPTUNE HAUSA: Ganin cewa akwai sana’o’i da yawa da mata suke yi, me ya sa kika zaɓi ki yi sana’ar Dambun Naman Kaji?

ZAINAB AQEELA: To gaskiya ba ni ne na na zaɓi na yi sana’ar dambun naman kaji ba, dambun naman kaji ne ya zaɓe ni tare da irshadin wani bawan Allah (dariya). Na fara wannan sana’a shekara uku da suka gabata. Asali na fara sana’ar dambun naman kifi ne. Don a lokacin da na fara sana’ar ma ba ni da ko sisi, naira hamsin tana matuƙar burge ni a wancan lokacin. Yadda abin ya faro shi ne, akwai wani bawan Allah da muke mutunci da shi. Mun haɗu da shi ne sanadiyyar auren wani ɗan’uwanmu da aka yi. Shi abokin ango ne. To dai shi ya kawo min kifi, bai ma wuce na ɗari bakwai ba. Shi ne na ce bari na fara sana’a da shi.

To da na yi dambun kifin sai na ɗora a Whatsapp na ce na fara sana’a, shikenan cikin ikon Allah, a haka dai aka yi ta aiko wa har kifi ya ƙare. To akwai wani da yake so na a wancan lokacin, shi ma yana sayan dambun kifin, to shi ne ya bani shawarar na fara dambun naman kaza. To gaskiya a lokacin har na ji haushinsa, saboda yaya za a yi ya ce na fara dambun naman kaza, bayan na kifin ya samu karɓu wa, idan na yi ƙare wa yake nan take. Sai na ce masa bani da jarin da zan fara dambun naman kaza. To sai ya ɗauki naira dubu biyar ya bani, to da ita dai na fara, kuma cikin ikon Allah, shi ma ya karɓu. Yanzu dambun naman kaji na yana shiga jihohi da dama a ƙasar nan.

NEPTUNE HAUSA: Da yake kina ɗora tallan dambun naman kajin naki a soshiyal midiya, ta yaya kike aika wa zuwa jihohi daban-daban?

ZAINAB AQEELA: Batun aika wa jihohi, dole na gode wa al’ummar jihar Kano. Domin gaskiya sune suka fara min ciniki a wata jiha. Daga mutum ya ce yana so, idan ya faɗi adadin da yake so, sai na ɗauka na kai tasha, na rubuta lambarsa, kuma nan da nan sai na ji mutum ya bugo yana cewa saƙonsa ya isa, har ya karɓa. Kuma sai ya ce dambun ya yi daɗi. To wannan yana ƙara min ƙarfin gwiwa. Kowace jiha ta mota nake aika musu, kuma Alhamdulillah, ban taɓa samun matsala a tura wa ɗin ba. Na samu alherai da yawa waɗanda ba zan iya lissafa su ba.

KU KUMA KARANTA: Sana’ar Dinki Na Da Bukatar Sadaukarwa Domin Biyan Bukatun Al’umma

NEPTUNE HAUSA: Ko kin taɓa samun tallafi daga gwamnati ko wata ƙungiya?

ZAINAB AQEELA: Eh to, tsohon gwamnan jihar Katsina, Alhaji Aminu Bello Masari, ya taɓa ba ni kyautar naira dubu ɗari da hamsin (150,000). Yadda abin ya faru shi ne, mun kai masa ziyara ne ƙarƙashin wata ƙungiya ta ƙananan ‘yan kasuwa masu fasaha ta musamman. Dalilin da ya sa ya ba ni kyautar wannan kuɗi shi ne, a lokacin da muka kai masa ziyarar, bayan ya fito, sai kowa ya gabatar da kansa. To da aka zo kaina na ce ina yin sana’ar dambun naman kaji, sai gwamnan ya ce “ina dambun naman yake?” sai na bayar aka miƙa masa. Take a wajen ya buɗe ya fara ci. Kuma wani ikon Allah ni kaɗai ce na je da abin sana’ata a cikinmu.

Gwamna da ya buɗe ya fara ci, sai ya miƙa wa sauran kwamishinoni da sakataren gwamnati. Haka dai aka cinye dambun da na je wajen da shi. Daman dambun naira dubu 18,000 ne. Gwamna ya ce dambun ya yi daɗi. Ya ce “ga daɗi ga araha” shi ne gwamnan ya bani naira dubu ɗari da hamsin (150,000) ya ce a ƙara jari. Amma in ban da wannan ban taɓa samun tallafi daga ko ina ba.

NEPTUNE HAUSA: To wane ƙalubale kike fuskanta a wannan sana’a ta ki?

ZAINAB AQEELA: Babban ƙalubalen da nake fuskanta a wannan sana’a shi ne ‘yan bashi. Sai ka ga mutum babba da girmansa, zai iya saya ya biya kuɗin, amma sai ya ce a aika masa zai turo kuɗin. Amma shiru ba zai turo ba. Kuma ina ganin girmansa ba zan iya hana shi ba. In har na tambaya sau biyu bai ba ni ba, to ba na sake tambaya. To ni wallahi babban ƙalubale na shi ne ‘yan bashi. Da a ce za su fahimci karɓar bashi, a riƙe kuɗin, ruguza mai ƙaramin jari yake, to da sun daina riƙe bashin.

NEPTUNE HAUSA: Wane ƙira kike da shi ga sauran ‘yan’uwanki mata waɗanda ba sa yin sana’a?

ZAINAB AQEELA: Ƙira na ga sauran ‘yan’uwana mata waɗanda ba sa sana’a shi ne, yana da kyau su sani cewa mu mata muna da buƙatu da yawa, ke ce sayan wancan, ke ce sayan wannan. Babu buƙatar sai na bayyana, duk mace ta san da haka. Ba kowane iyaye ba ne suke da ƙarfin da za su sayawa ‘ya’yansu dukkan waɗannan abubuwan. Amma idan kina sana’a kusan komai za ki yiwa kanki, kuma ba ki takurawa kowa ba. Irinsu anko da kayan kwalliya duk za ki yiwa kanki, ba sai kin damu wani da roƙo ba. Kin san roƙo yana zubar da daraja da mutunci, musamman mu mata. Babban abin da sana’a take buƙata shi ne, haƙuri, juriya da addu’a. Musamman addu’ar iyaye.

NEPTUNE HAUSA: Mun gode.

ZAINAB AQEELA: Ni ma nagode.

Leave a Reply