Sana’ar Dinki Na Da Bukatar Sadaukarwa Domin Biyan Bukatun Al’umma

0
503

Daga; ABDULMALIK JIBRIL, Kaduna.

SANA’AR Dinkin hannu wani aiki ne mai mahimmanci wanda al’umma suka dade suna yi domin neman rufin ashirin kansu ta hanyar dogaro da kai musamman a irin wannan lokaci na bukatar samun hanyoyi na dogaro da kai ta yadda zamantakewa za ta yi albarka.

Sai dai kamar yadda aka san ita wannan dadaddiyar sana’ar ta dinki wacce ba ta da shamaki na wariyar Jinsi, sana’a ce wacce ta kunshi kowace jinsin al’umma manya da kanana dukda cewa a wannan zamanin, matasa ne suka fi karfin a cikin harkar musamman maza da mata duk da cewa tana kunshe da wasu kalubale.

Hakazalika, idan aka yi la’akari da ita wannan sana’ar wacce ta kunshi galibin matasa wadanda ke aikin sadaukar da rayuwarsu domin jindadi da biyan bukatun sauran al’umma musamman a lokutan shagulgula irin na bikin Sallah da kirsimeti, za a iya ganin kalubalen dake tattare da ita musamman wajen cika alkawari a bangaren teloli.

Wakilinmu daya kewaya damin jin ta bakin wasu telolin da irin abubuwan da ke haifar da kalubalen da kunshe a cikin ta, ya gano cewa akwai rashen fahimta tsakanin masu aikin dinkin, wato teloli kenan da Jama’ar da suke wa aiki wanda haka ke haifar da sabani na rashin cika alkawarin dukda cewa mafi akasarin kowani bangaren na da ta su matsalar da ke haifar da damuwar.

Wani Matashin tela mai suna Hamisu dan kimanin shekara ashirin da biyu a duniya dake garin Kaduna, ya bayyana cewa ba laifinsu bane a mafi akasarin lokuta, face akasi ake samu yayin da wata matsalar daga ma’aikatar wutan lantarki ne, haka wani lokacin kuma daga masu kawo dinkin, amma dai su teloli suna iya bakin kokarinsu, kuma abin a jinjina musu ne.

Acewarsa, kamar a duk lokutan Azumin Ramadana musamman idan aka shiga gomar karshe, yayin da sauran al’ummar musulmi ke can su na neman lahirarsa, su kuma telolin suna nan suna hana idanuwansu barci domin su samar wa mutane suturar da zasu saka ranar sallah domin Biyan bukatunsu, amma a hakan dole sai an sabawa wasu saboda haka wannan wani abun a jinjinawa da yaba wa teloli masu sana’ar dinki ne.

Shi kuma wani tsohon tela mai suna Bala tela wanda ya kai kimanin shekaru ashirin yana sana’ar dinkin, ya bayyana cewa dalilan da yasa wasu teloli ke guduwa su shiga buya lokutan sallah, hakan na faruwa ne sakamakon amsar kayan da yafi karfinsu da su ke yi ne, duk da cewa wasu telolin na yin hakan ne ba da son ransu ba, face sai don wasu Jama’ar da su ke tilasta musu ne.

Ya ci gaba da cewa a wasu lokutan, matsalolin wutar lantarki da ake yawan samu a gari ne ke haifar da hakan don wani lokacin wasu telolin kan lissafa adadin kayan da zasu iya yi a rana amma kuma matsalar wutan na kawo tsaiko wajen gudanar da ayyukan wanda har hakan ke kaiwa ga zama rashin ciki alkawari daga bangaren telolin.

Sannan ya kara da cewa mafi akasarin wadanda ake kin yi musu dinkin, wani lokacin su ma suna da irin tasu matsalar ta kin kawo dinkunansu da wuri ko kin biyan kudin aikinsu a kan lokaci wanda ta hakan ke sanya wasu mutanen ke neman mayar da wasu telolin tamkar bayi ko maroka saboda hakkinsu na gagarar a biya su.

Idan za a iya tunawa dai, ita wannan sana’a ta aikin dinkin tela, sana’a wacce iyaye da kakannin kakanni suka jima suna yin ta kuma sana’a ce ta rufin asiri ga duk wanda ya rike ta daraja, mutunci kuma ya yi gaskiya a cikin ta, kana ya dauke ta a matsayin hanyar neman halak din shi ko tafiyar da rayuwar shi.

Leave a Reply