Yadda Kananan Yara Suka Kware Wajen Hada Abin Makala Makullai A Kunnawa Majema

0
401

JABIRU A HASSAN, Daga Kano.

SANA’AR hannu tana da matukar muhimmanci ga al’umma musamman a wannan lokaci na bukatar samun hanyoyi na dogaro dakai ta yadda zamantakewa za ta yi albarka.

A garin Kunnawa Majema, yankin Karamar hukumar Dawakin Tofa, wakilin mu ya ruwaito yadda kananan yara suka kware wajen hada abin makala makullai watau (Key Holders) a matsayin sana’ar su ta samun rufin sutura.

Kusan dukkanin inda albishir ta zagaya, akwai rukuni-rukuni na yara wadanda shekarunsu suka kama daga biyar zuwa ashirin suna sana’ar hada abin makala makullai bisa kwarewa da fasaha domin aikawa dasu wasu sassan wannan kasa harma da kasashe makwabta.

Sannan akwai yara dake daukar wadannan abubuwa zuwa kasuwanni na Jihar Kano har da wasu Jihohin wanda hakan ta sanya yara kanana da matasan garin Kunnawa Majema suka kasance masu dogaro da kai ta fuskar sana’ar hannu.

Mafiya yawan mutanen da wakilin mu ya yiwa tambayoyi kan wannan sana’a ta hada abin makala makullai watau (Key Holders), sun sanar da cewa akwai alheri cikin wannan sana’a, sannan yara da sauran mutane masu yin ta sun kasance cikin yanayi mai kyau.

Malam Yusuf Sa’ad, ya yi karin haske dangane da sana’ar hada abin makala makullai watau (Key Holders) inda ya nunar da cewa ko shakka babu, wannan sana’a tana da kyau duba da yadda ta ke samar da aiyukan yi ga al’umma musamman yara kanana.

Ya yi kira ga mahukumta da sauran masu ruwa da tsaki kan harkar cinikayya da kasuwanci da su yi kokarin tallafawa masu sana’ar hada abin makala makullai da sauran sana’o’i da suka shafi harkar a Kunnawa Majema, tare da jaddada cewa za su ci gaba da assasa dukkanin wata sana’a da za ta bunkasa tattalin arziki da dogaro da kai a wannan yanki.

Leave a Reply