Daminar Bana: Takin Namalale Ya Ciri Tuta Ga Manoman Najeriya

0
374

Daga; Rabo Haladu.

A DAI-DAI lokacin da daminar bana ta fara kankama, wata Kamfanin samar da takin zamani na Namalale dake jihar Kano a Arewacin Najeriya, ya himmatu wajen ganin ya samar da taki mai inganci da nagarta ga daukacin manoman Najeriya baki daya.

Kamfanin Namalale, ya bada tabbacin cewa suna samar da taki wanda ya yi daidai da yanayin kasar noman da ake da ita a Najeriya bisa farashi mai sauki.

Kamfanin, ya kara da cewa ga masu bukatar samun takin suna iya zuwa hedikwatar Kamfanin dake kwanar Laraba kan Titin Hadejia a karamar hukumar Gezawa dake jihar Kano.

A ta bakin Manajan Kamfanin Umar Sallau Musa, yace Kamfanin ya dukufa wajen tabbatar da cewa ya samar da takin zamani a lokacin bukatarsa daga Kano zuwa wasu jihohi dake fadin Najeriya ga masu bukata.

Manajan Kamfanin ya bukaci duk masu neman takin na Namalale suna iya tunkarar kasuwanninsu, kuma a kan hakan Kamfanin ya bukaci masu hulda da takin su da su kaucewa sayan kayansu ga gurbatattaun dillalan takin masu yin algus, hasalima, Kamfanin yana Maraba da duk masu bukatar takin su a duk inda suke, inda yace takin Namalale shi ne zabin manoman Najeriya.

Leave a Reply