Dalilin da ya sa na saka wa matata sasari – Wani magidanci a Potiskum

0
1841

Daga Ibraheem El-Tafseer

A ranar Laraba ne, labarai suka karaɗe kafafen yaɗa labarai a kan wani magidanci ya saka wa matarsa sasari (ankwa) a garin Potiskum ta jihar Yobe. Wannan labarin ya sa mutanen unguwar suka fita don bincika haƙiƙanin labarin. Bayan sun tabbatar da labarin, sai suka garzaya wajen jami’an tsaron ‘Nigerian Security and Civil Defence Corps’ (NSCDC), inda aka je gidan aka kamo shi a cikin daren, suka kwana a ofishin NSCDC na Potiskum.

Da safe aka fara yi masa tambayoyi a ofishin NSCDC da ke Potiskum. Shi wannan magidanci sunansa Malam Muhammadu mai waldar Robobi, inda ya bayyana cewa dalilin da ya sa ya saka wa matar tasa sasari shi ne, ita matar tasa tana fita bara, sannan tana da taɓin hankali. Amma ita matar ta musanta.

KU KUMA KARANTA: An kama mijin da ya saka wa matarsa sasari a Potiskum

Kwamishinar harkokin mata ta jihar Yobe ta zo musamman don binciken haƙiƙanin abin da ya faru aka saka mata sasari. Ƙungiyar ba da agaji ta SEMA, ita ma halarci gidan matar.

Ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan adam daga Yobe da jihar Borno duk sun halarci gidan matar da abin ya faru. Kakakin NSCDC a jihar Yobe, Bala Garba ya shaida wa manema labarai cewa, “jama’ar unguwa ne suka kawo mana kukan abin da yake faruwa na matar da aka saka mata sasari, inda muka tura jami’anmu don bincika wa. Kuma suka taho dasu duka. Zuwa yanzu ana yi masa bincike”.

Rahotanni mabambamta sun yi ta bayyana daga baya, inda aka ce, an tabbatar da cewa wannan mata tana fama da taɓin hankali, wataran ma idan ta fita ba kwana take a can, shi ya sa aka ɗaure ta. Amma kuma ita matar da kanta ta musanta wannan zargi. Ta ce idan ta fita bara ɗinma, idan ta dawo, shi mijin ne yake karɓar kuɗin.

Zuwa haɗa wannan rahoto, wannan magidanci yana hanun hukumar ‘yan sanda a garin Damaturu, ana ci gaba da yi masa bincike.

Leave a Reply