‘Yan Najeriyan Da Suke Son Yin Hijira Daga Kasarsu

  0
  596

  Daga Wakilinmu

  Woman waving

  Cikin jerin wasikun da muke wallafa wa daga marubutan Afirka, marubuciya Adaobi Tricia Nwaubani daga Najeriya ta duba karuwar damuwa tsakanin ‘yan kasar masu dan abin hannunsu da ke sa su fice daga kasarta.

  Wasu shekaru da suka gabata, wata kawata wadda tun muna yara muke tare ta komo Najeriya bayan ta shafe shekaru fiye da 20 a Amurka tana karatu da aiki.

  Amma duk da cewa ta sami aiki a wani babban kamfani a Legas, kuma tana samun albashi mai tsoka, sannan tana da gida a unguwar masu abin hannunsu da ke gundumar Lekki, ba da dadewa ba sai ta ce za ta kwashe kayanta ta koma Amurka.

  “Mutane na nuna min tamkar cewa akwai wata lada da ake ba wanda ya iya zama a Najeriya,” kamar yadda ta gaya min. “Ni ba ni da ra’ayin karbar wannan lambar yabon.”

  Tana da gaskiya da ta ce yawancin mu da ke iya samun ci gaba a Najeriya na kallon lamarin a matsayin wata jarumta ta musamman.

  Idan muka tafi kasashen waje, ‘yan Najeriya da suka bar kasar na kallon mu da al’ajabi yayin da muke kokawa da kayanmu a filayen jirgin saman kasashen.

  Sukan yi mamakin cewa muna farin cikin komawa kasar da ta yi kaurin suna saboda matsaloli kamar rashin cimma buri da rashin yanayin bin doka da oda da gwagwarmayar rayuwar yau da kullum a nan.

  Sukan ce “Ba zan iya tunanin yadda kuke iya rayuwa a kasar nan ba. Kuna kokari sosai”

  Sai dai ciin ‘yan kwanakin nan, akwai karin ‘yan Najeriya da ke yanke hukuncin da ke cewa ba sa bukatar a ci gaba da yaba mu su saboda jurewar da suke nunawa ta rayuwa a kasar.

  ‘Yan Najeriya bakwai cikin 10 na son ficewa daga kasarsu idan ska sami damar yin haka, kamar yadda wani rahoto da cibiyar Africa Polling Institute ta wallafa a 2021.

  A shekarar 2019, irin wannan binciken ya nuna cewa kashi 32 cikin 100 na ‘yan najeriya ne ke son barin kasar.

  Yawancin kasashe na bukatar a duba lafiyar ‘yan Najeriyan da ke neman zama na lokaci mai tsawo ko kuma masu son yin hijira baki daya.

  A watan Janairun 2022, ‘yan Najeriya kan shafe sa’o’i 10 kafin a sami daukan hoton X-ray a ofishin hukumar kula da ‘yan gudun hijira da ke Legas, inda a Abuja kuwa sai sun yi jiran sa’o’i shida. Duka-duka minti uku kawai ake dauka wajen daukan hoton.

  “Ba mu taba ganin irin wannan kwararar jama’a ba kamar yadda muke gani tun bara,” kamar yadda wani likitan hukumar ya sanar da ni amma a fakaice domin ba ta son a bayyana sunanta.

  “Idan lamarin ya ci gaba, tilas mu dauki matakai domin sauwaka wahalar da ake sha.”

  A money changer flicking through notes
  Bayanan hoto,Faduwar darajar naira na cikin dalilan da ke sa ‘yan Najeriya ke neman barin kasar

  Babu abin da ke rage kaifin kokarin ficewa daga Najeriya da ‘yan kasar ke yi. Ko annobar korona da yawan alkaluman masu kamuwa da cutar ba su iya taka mu su birki ba.

  Cibiyoyin da ke sarafa masu neman bizar shiga kasashen waje sun kasance cike da jama’a a daidai lokacin da annobar ta fi kamari, har ta kai ga tsawon layukan masu neman bizar na kai wa wajen ginin.

  Sai dai abin lura shi ne ba kamar a baya ba da yawancin masu son tserea daga Najeriya talakawa ne da ba su da aikin yi kuma ba su da karfin gwuiwar samun sauki daga matsin rayuwa nan kusa, inda yawancin masu ficewa a yanzu daga cikin ‘yan kasar masu rufin asiri ne.

  Domin su guje wa sanar da wadanda suka dauke su aiki cewa suna son barin kasar, saboda haka dukkan wadanda na yi hira da su sun bukaci in sakaya sunansu.

  Halin da ‘yan kasar ke ciki sai kara ta’azara yake yi cikin shekarun da suka gabata kuma mutane na da dalilai mabanbanta kan dalilansu na son barin kasar.

  Wasunsu sun yi imanin kasar ba ta da abin da za su iya rayuwa a kai. Wasu kuwa sun damu ne da yadda takardar kudin kasar wato naira ke rasa darajarta.

  Dala daya ta Amurka daidai ta ke da naira 198 a lokacin da Shugaba Muhamadu Buhari ya zama shugaban kasar shekara bakwai da ta gabata. A yau kana bukatar naira 572 ne kafin ka yi musayar su da dalar Amurka daya a kasuwar bayan fage.

  “Na kan yi tunani ina samun albashi mai tsoka,” inji wani manajan banki. “Amma idan dai a naira ake biya na, dukkan abin da na adana, ko mai yawansa, na iya rasa darajarsa baki daya nan da gobe.”Nigerian passportsGetty ImagesNigeria is easier to bear when you know that you can press the eject button and leave whenever you want. The problem is when you feel that you are stuck here.”Nigerian lawyer

  A farkon shekarun 1980, lokacin da tattali arzikin Najeriya ya fara shiga matsala, yawan masu tserewa daga kasar ya kai ga sai da gwamnatin Janar Muhammadu Buhari a wancan lokacin ta rika yin tallace-tallace a rediyo da talabijin domin jan hankalin ‘yan kasar su zauna a gida domin gina kasar.

  Akwai wani talla mai farin jini, wanda a cikinsa wani mutum mai suna Andrew ke jan jakarsa a wani filin jirgin sama, yayin da yake furta tarin matsalolin da ke damunsa da Najeriya.

  Ya ce: “Zan yi waje ne! Na gaji!

  Daga nan sai wani mutum ya dora masa hannu a kafada.

  “Andrew! Kar ka fice!”

  Wannan mutumin mai kishin kasa da ya hana Andrew ficewa ya ci gaba da zayyana wasu abubuwa masu karfafa zuciya game da makomar Najeriya, kuma a karshe Andrew ya fasa ficewa daga kasar.

  Sai dai a yanzu da alma Muhammadu Buhari, wanda shugaban zababbiyar gwamnatin demokradiyya ne, bai damu da yawan ‘yan kasar da ke ficewa daga kasar tasa ba.

  “Ga duk wanda yake ganin yana da wata kasar da ta fi Najeriya: Sai wata rana,” kamar yada yace cikin wani jawabin da ya yi a 2019.

  “Kana iya tafiya, amma za mu yi zamanmu a nan. Mun jajirce domin sake gina kasarmu, musamman domin amfanin ‘ya’yanmu da jikokinmu.”

  Leave a Reply