Matsirga Waterfalls, Kaduna, Najeriya

2
184

Matsirga Waterfalls, wani magudanar ruwa ne da ke Batdon, wani ƙaramin ƙauye ne a gundumar Advwan, a masarautar Fantswam, a yankin Kafanchan, a kudancin jihar Kaduna, da ke Arewa maso yammacin Najeriya.

Ruwan ya samo asali ne daga maɓuɓɓugan da ke kan tsaunin Kagoro, zuwa wani kwazazzabo da ke kewaye da duwatsu wadda suka gangamo daga ramuka guda huɗu na dutsen da ya kai kimanin mita 25, suka kuma samar da wani babban tafki a gindinsa.

Mazauna yankin sun kwatanta magudanan ruwa na Matsirga a matsayin “Abin Alfahari da Sha’awa.”

Yanayin wurin ya na sanyi wadda yake samar da natsuwa da kyan gani ga masu yawon shaƙatawa.

2 COMMENTS

Leave a Reply