Labarin yana gefen ku!

Kannywood ta ba wa Hisbah tabbacin goyon baya a Kano

1

Bayan ce-ce-ku-ce, Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta sake zama da daraktoci da furdusoshi da jarumai da sauran masu ruwa da tsaki a Kannywood don tsaftace harkar fim da nufin kau da ayyukan baɗala a jihar.

A jawabansu daban-daban, Shugaban Ƙungiyar MOPPAN ta Ƙasa Dokta Ahmad Sarari da takwaransa na Jihar Kano Ado Ahmad Gidan Dabino da Shugaban Ƙungiyar Jarumai Alasan Kwalle sun nuna jin daɗinsu game da taron inda suka sha alwashin ba wa Hisbah goyon baya tare da alkawarin cewa nan gaba za a samu gyara a harkar fim ɗin.

Wannan shi ya kawo ƙarshen ce-ce ku-cen da aka yi ta yi game da ganawar Hukumar da ’yan fim na farko, wanda mafi yawansu suka ƙaurace wa bisa hujjar cewa Hisbar ba ta bi hanyar da ta dace wajen gayyatar su ba.

KU KUMA KARANTA: ’Yan Kannywood da dama sun ƙaurace wa taron da Hisbah ta gayyata a Kano

Hukumar ta sake miƙa musu goron gayyata a karo na biyu wanda suka amsa a ƙarƙashin jagorancin ɗan gidansu wato Shugaban Hukumar Tace Finafinai da Dab’i ta Jihar Kano Abba Almustapha.

Kwamanda-Janar na Hukumar Hisbah Shaikh Aminu Ibrahim Daurawa ya bayyana cewa ƙorafe-ƙorafe da suke yawan samu daga Kanawa da sauran sassan Najeriya kan yadda ’yan fim ke nuna abubuwan da suka saɓa wa addinin Musulunci da al’adun Hausawa a cikin finafinansu ya sa suka ga dacewar zama da masu ruwa da tsaki a harkar fim don laluɓo hanyoyin kawo gyara a cikin harkar.

“Ita Hukumar Hisbah an kafa ta ne don ta saita al’umma a kan koyarwar addinin tare da yi musu katanga daga aikata munanan ayyuka.

“Muna so a laluɓo hanyoyin da za a rage nuna abubuwa da suke na tir tare da ci gaba da nuna abubuwa da za su dabbaka addinin da kyawawan koyarwar al’adun Hausawa a harkar fim,” in ji Daurawa.

A nasa ɓangaren, Abba Almustapha ya bayyana cewa tuni ’yan fim din suka amince za su zama masu bin doka.

Abba Almustapha ya jaddada cewa nan ba da dadewa ba hukumomin biyu za su shirya taron ƙara wa juna sani da ’yayan Kannywood don ilimintar da su kan abin da ya shafi fim ta fuskar addinin Musulunci inda za a gayyato fitattun malaman Musulunci don tattauna tare da laluɓo hanyoyin da za a kai harkar fim ɗin ga tudun mun tsira.

Leave A Reply

Your email address will not be published.