Ɗan Ghana ya kafa tarihi na rungumar bishiyoyi a duniya

0
71

Wani ɗalibi ɗan gwagwarmayar kare muhalli da gandun daji a Ghana ya kafa tarihin rungumar bishiyoyi masu yawa cikin sa’a ɗaya.

Kundin Adana Kayan Tarihi na Guinness ya wallafa a shafinsa cewa Abubakar Tahiru, mai shekara 29 ya rungumi bishiyoyi 1,123 cikin sa’a guda.

Abubakar ya taso ne a garin Tepa da ke albarkatun noma a Ghana, inda ya samu sha’awar abubuwan da suka shafi gandun daji da yanayi.

KU KUMA KARANTA:Ƙasashen Ghana da Kenya sun rattaɓa hannu kan yarjejeniyar haɗin gwiwa

Bayan kammala karatunsa na digirin farko a fannin gandun daji a ɗaya daga cikin manyan jami’o’in Ghana, Abubakar ya ci gaba da karatu a fannin gandun daji a jami’ar Auburn da ke jihar Alabama da ke Amurka a shekarar da ta gabata.

Ya kafa tarihin ne a gandun dajin Tuskegee, ɗaya daga cikin manyan gandun daji mai albarkatun bishiyoyin timber da ake katako da ita, a jihar ta Alabama.

Yadda yake rungumar bishiyoyin shi ne yakan rungume duka hannayensa a jikin bishiyar, kuma babu bishiyar da ya runguma fiye da sau ɗaya, kuma babu wata illa za dai yi wa bishiyar sakamakon rungumar.

Leave a Reply