Ƙasashen Ghana da Kenya sun rattaɓa hannu kan yarjejeniyar haɗin gwiwa

0
88

Shugaban ƙasar Ghana, Nana Akufo-Addo da na Kenya, William Ruto, sun shaida hakan inda Ministar harkokin wajen Ghana, Shirley Ayorkor Botchwey, da sakataren majalisar ministocin harkokin wajen Kenya, Dokta Musalia Mudavadi, suka jagoranci rattaɓa hannun kan yarjejeniyar diflomasiya a fadar shugaban ƙasa, Jubilee House, da ke birnin Accra.

Ƙasar Ghana da Kenya sun ƙara haɓaka hulɗar diplomasiya da tattalin arziƙi, ta hanyar tattaɓa hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna da za ta tabbatar da haɗin gwiwa tsakanin ƙasashen biyu da burin nemo hanyoyin da ƙasashen za su bunƙasa hulɗar kasuwanci, tattalin arziƙi da zamantakewa a tsakaninsu. Kasashen biyu sun rattaɓa hannu kan wasu yarjeniyoyi 7 da suka haɗa da ilimi, yawon buɗe ido, tsaro, da inganta zuba jari, masana’antu, ƙere-ƙere da kasuwanci, a yayin ziyarar kwanaki uku da shugaban ƙasar Kenya, William Ruto, ya kai zuwa Ghana.

Haka kuma an rattaɓa hannu kan wasu yarjeniyoyi da suka haɗa da ilimi, yawon bude ido, hadin gwiwa kan tsaro, kasuwanci da zuba jari, masana’antu da gudanar da mulki domin karfafa alaƙar dake tsakanin ƙasashen biyu.

KU KUMA KARANTA:Kenya ta sha alwashin kawo ƙarshen yaƙin Gang na Haiti

A wani taron manema labarai na haɗin gwiwa, shugaba Akufo-Addo ya ce, ‘Hulɗar kasuwanci da tattalin arziƙi tana ci gaba da bunƙasa a tsakanin ƙasashen Ghana da Kenya, inda ƙasashen biyu ke ƙara fahimtar juna da kuma nuna goyon baya ga juna a ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa da suka haɗa da Majalisar Ɗinkin Duniya, Tarayyar Afirka, da ƙungiyar ƙasashen renon Ingila, na Commonwealth’.

A nasa ɓangaren Shugaba Ruto ya bayyana cewa, ‘yancin zirga-zirgar jama’a tsakanin Ghana da Kenya ya haifar da fa’ida sosai a fannin kasuwanci, zuba jari, da kuma yawon buɗe ido.

“A dangane da haka, ni da mai girma shugaban ƙasa, mun lura cewa, kasuwanci tsakanin Kenya da Ghana ya bunƙasa a shekarar 2022, misali, a shekarar 2022, Kayayyakin da Kenya ta shigo da su cikin Ghana sun kai na dalar Amurka miliyan 10.4, kuma an ƙiyasta wasu kayayyakin da ake shigo da su a kan dalar Amurka miliyan 4.8.”

Wani mai sharhi kan harkokin siyasar cikin gida da ƙetare, Malam Issah Abdul Salam yace, sakamakon alaƙa da aka ɗora tsakanin Ghana da Kenya, ya sa shugaba William Ruto ya zo Ghana don ƙara jaddada alaƙa mai kyau da ke tsakanin su tun da jimawa. Kuma wannan ziyarar za ta aka ƙara bunƙasa sha’anin, ‘ilimi, yawon buɗe ido da ba da dama ga ziyarar ƙasashen juna, abubuwa ne da za su samar da mafani masu ɗimbim yawa tsakanin Ghana da Kenya”.

Masani kan harkokin kuɗi da kasuwanci, Hamza Attijjany, yace ƙasashen biyu za su amfana ta ɓangaren tattalin arziƙi, musamman a kasuwanci da ba shi da shinge tsakanin ƙasashen Africa, da ƙasar Ghana da Kenya suka runguma da hannu biyu-biyu. Yace, ‘A lokacin da ƙasar Kenya ta fara yin batir, Ghana ce ƙasa ta farko da aka fara yiwa talla don kasuwanci. Lallai Ghana da Kenya za su samu ci gaban tattalin arziƙi da ma nahiyar Afirka baki ɗaya’.

Al’ummar ƙasashen biyu, za su samu alfanu idan an tabbatar da waɗannan yarjejeniyoyin, in ji mai sharhi kan al’amuran yau da kullum, Malam Issah Mairago Gibril Abbas, wanda yace ɗaliban ƙasashen biyu za su samu damar zurfafa iliminsu ta hanyar yarjejeniyar; haka kuma ‘yan kasuwar ƙasashen za su ci moriyar shirin nan na cinikayya tsakanin ƙasashen Afrika mara shinge AfCFTA.

A yayin ziyarar shugaba Ruto, ta kwanaki ukun, ya ba da lecca a hedkwatar AfCFTA ya kuma ziyarci kabarin tsohon shugaban Ghana, Kwame Nkrumah, a birnin Accra. Daga bisani Ghana ta karrama shi da babbar karramawa mai daraja, wato Companion of the Order of the Star of the Volta.

Leave a Reply