An haramta shirya fina-finan da ke nuna ƴan daudu da ƴan daba a Kano

0
106

Hukumar tace fina-finai ta Kano ta haramta shirya fina-finai da ke nuna faɗan daba da harkar Daudu a Kano.

Shugaban hukumar Abba El-Mustapha ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da hukumar ta tace fina-finan ta fitar a ranar Laraba.

Hukumar ta ce ta ɗauki wannan mataki ne bayan ta tattauna da ma’aikatan hukumar da wasu daga cikin wakilan yan masana’antar shirya fina-finan ta kannywood waɗanda suka haɗa da ƙungiyoyin MOPPAN, Arewa Film Makers da daraktoci da kuma furodusoshi.

Abba ya ƙara da cewa doka ce ta bai wa hukumar damar dakatarwa ko hana duk wani film da take ganin ya ci karo da tarbiya tare da al’adar al’ummar da ke jihar.

KU KUMA KARANTA: Kannywood ta ba wa Hisbah tabbacin goyon baya a Kano

“Tuni lokaci ya shige da za’a saka ido irin wannan gurbatattun fina-finai su ci gaba da yaɗuwa a cikin al’umma,” in ji shi.

Ko a kwanakin baya sai da hukumar ta ɗauki matakin rufe gidajen gala a jihar inda ta ce har sai bayan azumin watan Ramadana.

Leave a Reply