Labarin yana gefen ku!

IPMAN ta yi barazanar rufe gidajen mai 30,000

1

Daga Idris Umar, Zariya

Dillalan mai a ƙarƙashin ƙungiyar dillalan man fetur mai zaman kanta ta Najeriya, IPMAN a jiya Talata, sun bayyana cewa za su rufe gidajen mai guda dubu 30 da ‘yan ƙungiyar IPMAN ke gudanarwa a faɗin ƙasar nan idan har gwamnatin tarayya ta gaza biyan su bashin Naira biliyan 200 da su ke bin gwamnati.

IPMAN ta ce musamman hukumar kula da harkokin man fetur na ruwa da tsandauri ta Najeriya, NMDPRA ta ƙi yafe basussukan da ke ci gaba da ƙaruwa tun watan Satumban 2022.

Ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da shugaban ƙungiyar ta IPMAN reshem tashoshin ɗakin mai, Yahaya Alhassan ya fitar a Abuja, kan rashin biyan kuɗaɗen da ‘yan kasuwa ke bi ya ce IPMAN tana kula da gidajen mai sama da dubu 30 a Najeriya.

Su waɗannan kuɗaɗe diyya ne da gwamnati ke yi biya wa ‘yan kasuwar man don jigilar man fetur da aka yi lodi daga gidajen man fetur zuwa jihohi daban-daban a faɗin ƙasar nan.

Alhassan ya ce sakamakon gazawar da hukumar ta NMDPRA ta yi na biyan Naira biliyan 200 “zai yi muni matuƙa, domin duk wani gidan mai da ke faɗin Najeriya, daga Arewa zuwa Kudu, daga Gabas zuwa Yamma za a rufe.

KU KUMA KARANTA: NNPCL ya ɗora alhakin ƙarancin man fetur akan matsalolin tsare-tsare

Ya ƙara da cewa, “A matsayinmu na ƙungiyar IPMAN, mun ɗauki kowane mataki a baya don ganin mun ceto wannan al’amari mai cike da ban tausayi, wanda kuma mun san ba zai yi wa ‘yan Nijeriya daɗi ba, amma a halin yanzu ba mu da wani zaɓi da ya wuce mu fita gaba ɗaya a cikin ‘yan kwanaki kaɗan masu zuwa, don magance wannan mummunar ɗabi’a ta hanyarmu, wanda zai haifar da wahala da haɗari ga ‘yan Najeriya,” in ji shi.

Ya zuwa fitar da wannan saƙo da yawan jama’a cikinsu ya ɗibi ruwa bisa tunanin halin da za a shiga.

Leave A Reply

Your email address will not be published.