Labarin yana gefen ku!

An kama mai garkuwa da mutane a Kogi

1

An kama wani mai garkuwa da mutane mai shekaru 43 a ƙauyen Ofodo da ke kusa da garin Egabada a Karamar Hukumar Igalamela-Odolu ta Jihar Kogi.

Jami’an tsaro da ’yan banga ne suka kama shi a ranar Litinin, inda suka same shi da bindiga tare da wasu abubuwa da ake tuhuma da suka haɗa da laya.

KU KUMA KARANTA: Ƴan bindiga sun yi garkuwa da ɗalibai da dama a jihar Delta

Wanda ake zargin dan asalin ƙaramar hukumar Bida ne ta jihar Neja, a cewar shugaban ’yan banga a yankin, Mohammed Ajitata.

Mohammed ya ce ɗan bindigar ya amsa laifin, kuma ya yi zargin cewa wani mutum dan kauyen Shanawa da ke karamar hukumar Lokoja ta jihar Kogi ne abokin aikinsa.

“Muna bin sa tun lokacin da muka gano motsin miyagun laifuka a unguwar Egabada-Odolu; ranar litinin, kuma muka ga kama shi a wani samame na hadin gwiwa,” in ji shi.

Kakakin rundunar ’yan  sandan jihar Kogi, SP Williams Aya, wanda aka tuntuɓe shi a kan lamarin ta hanyar sakon tes da kiran waya bai amsa ba.

Leave A Reply

Your email address will not be published.