Fahimta fuska

0
332

Mutane suna kallonsa a mahaukaci, hakan yasa nayi mamaki ganin ya matso kusa dani yana cewa ” Ina da ƴar tambaya, zan iya yi miki?”

Sai na gyaɗa kai, alamar “eh” kenan. Se yace ” Shin ni mahaukaci ne?”
Sai na amsa masa da “A’a” , wannan ita ce amsar da kowanne me hankali zai bayar. Sai yace min “Ya gode”.
Ya kara da cewar “Kawai don bana kallon abu ta fuskar da sauran mutane suke kalla, hakan yana nufin ni mahaukaci ne?”


Na ƙara bashi amsa da “Aa”.
Sai ya durƙusa kasa ya rubuta harafin “W”, yacemin “Me ya rubuta?” Amma a dai-dai wannan lokacin na kasa sakewa, saboda jin kunya na ɗaukar tsawon lokaci ina musayar kalamai dashi.


Cikin sauri se nace masa harafin “W” ne, Nayi mamaki sosai da jin irin martanin da yayimin. “Kina ganinta a “W” ne kawai saboda kusurwar da kike tsaye”. Da zaki juya sama ta dawo kasa, zaki ganta ne a harafin “M”, in kika juyata kuma ta kalli hagu zaki ganta a matsayin harafin “3”, haka ma in ta kalli dama zaki ganta a harafin “E”.

   "Don haka, Kawai don bana ganin abu ta fuskar da kake kallonsa ba shine yake nuna cewar ni mahaukaci bane."

Ya juya yaci gaba ta tafiyarsa.


Kafin ka zagi mutum, ko kayi masa wani kallo akan wani abu da ra’ayinku ya banbanta, ka tabbatar kayiwa kanka wannan tambayar. Shin a wanne gurbi nake kallon abu kaza? Shima ta wannan fuskar yake gani? Da wannanne zaka iya alkalanci na haƙiƙa ba tare da son kai ya shiga tsakiya ba.

Daga : Malam North

Leave a Reply