Connect with us

Siyasa

Tinubu/Shettima: Wannan tikitin babbar nasara ce ga Jam’iyyar APC – Gwamna Buni

Published

on

Gwamna Mai Mala Buni, na Jihar Yobe ya taya dan takarar shugaban ‘ƙasa na Jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, murnar zabar wanda ya cancanta ya zama mataimakin shugaban ƙasa, kana ya bayyana zabin Sanata Kashim Shettima babbar nasara ce ga Jam’iyyar APC.

Gwamnan wanda shi ne tsohon shugaban kwamitin riko na Jam’iyyar APC, ya bayyana tikitin Tinubu/Shettima a matsayin tikitin nasara ga jam’iyyar. Ya ce zaben Shettima, zai wadatar da dimbin magoya baya ga Jam’iyyar da kyakkyawar damar samun nasara a babban zaben 2023.

“Haɗin kai da Tinubu da Shettima ya sa Jam’iyyar ƙarin ƙarfin tunkarar zaɓen shugaban ƙasa a shekara mai zuwa tare da samun nasara a fili” in ji shi. Gwamna Buni ya ce ‘ɗan takarar shugaban ƙasa da mataimakinsa na jam’iyyar APC, mutane ne da ke da dimbin gogewa a harkar mulki domin ganin Najeriya ta samu ci gaba.

“Kwarewarsu na gudanarwa, kwarewa da labaran nasarori sun shirya su yadda ya kamata domin shugabancin ƙasar nan.” Najeriya zata samu ɗimbin nasarori da ɗimbin riba daga gwamnatin Tinubu/Shettima idan aka zabe su a ofis” inji shi.

Gwamnan ya ba da shawarar cewa a wannan mawuyacin lokaci na taɓarɓarewar tattalin arzikin duniya, Najeriya na bukatar kyakkyawar hadin kai da gogewa irin ta Tinubu da Shettima. Ya kuma bukaci jam’iyyar da ta ci gaba da kasancewa da hadin kai tare da mai da hankali wajen samun nasara a zaben 2023.

Gwamnan Jihar Yobe ya lura cewa Tinubu da Shettima suna mutunta duk wani addini, wanda hakan ya sa
Tikitin Musulmi-Musulmi ya fi karɓuwa saboda, dukkansu suna da juriya na addini, suna aiki da zama tare da mutane daga addinai daban-daban.

Gwamna Buni ya ce “APC tana da mutane sama da miliyan 40 da yardar Allah za ta lashe zaben 2023 bisa gaskiya da adalci.

2 Comments

2 Comments

  1. Pingback: Na daina jin daɗin rayuwa, jiran lokacin mutuwa nake- Aminu Ɗantata | Neptune Prime Hausa

  2. Pingback: Abin da yasa daraktar yaƙin neman zaɓen Tinubu, Naja’atu Mohammed, ta fice daga APC | Neptune Prime Hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Siyasa

APC ta dakatar da ɗan Majalisa kan cin amana a Zamfara

Published

on

APC ta dakatar da ɗan Majalisa kan cin amana a Zamfara

Jam’iyyar APC reshen Jihar Zamfara ta dakatar da Ɗan Majalisar Wakilai, Aminu Jaji bisa wasu zarge-zargen da ake yi masa na cin amanar jam’iyyar.

Sakataren Yaɗa Labarai na Jam’iyyar APC na Jihar, Malam Yusuf Idris ne ya sanar da dakatarwar a wani taron manema labarai a Gusau a ranar Juma’a.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa, Jaji yana wakiltar mazaɓar Ƙaura-Namoda/Birnin-Magaji a Majalisar Wakilai a ƙarƙashin jam’iyyar APC.

Idris ya ce wasu zarge-zargen da ake yi wa Ɗan Majalisar sun haɗa da aikata rashin gaskiya da rashin zuwa tarurrukan jam’iyyar da kuma sauran ayyuka.

KU KUMA KARANTA: Kotun Najeriya ta bayar da umarnin dakatar da asusun banki fiye da dubu 1

Ya ce, matakin ya biyo bayan sanarwar dakatarwar da aka yi wa Jaji daga shugabannin jam’iyyar APC na mazaɓar Birnin-Magaji bisa zargin cin amanar jam’iyyar da dai sauran abubuwan da suka saɓa wa jam’iyyar.
Idris ya ce, “Kwamitin zartaswa na jam’iyyar APC na ƙaramar hukumar Birnin Magaji ne ya miƙa sanarwar dakatarwar zuwa hedikwatar jam’iyyar APC ta jihar.

Bayanai sun ce kwamitin zartaswar jam’iyyar APC na jihar ya gudanar da taron gaggawa a sakatariyar jam’iyyar da ke Gusau a ranar Juma’a 17 ga watan Mayu, 2024, inda aka gabatar da batun dakatar da Jaji ga ‘yan majalisar zartarwar jihar.

Continue Reading

Labarai

Tsohon gwamnan Katsina, Shema ya sauya sheƙa zuwa APC

Published

on

Tsohon gwamnan jihar Katsina, Ibrahim Shema, a hukumance ya koma jam’iyyar APC Mai mulki a jihar.

Shema, ya kasance gwamnan jihar a tsakanin shekarar 2007 zuwa 2015, a ƙarƙashin jam’iyyar PDP.

Tsohon gwamnan ya yi rajista ne a ofishin jam’iyyar na mazaɓar Shema, ƙaramar hukumar Dutsin-ma, inda shugaban jam’iyyar na jihar, Sani Aliyu-Daura ya ba shi katin zama ɗan jam’iyyar APC.

Lambar katin Shema ta zama ɗan jam’iyyar ita ce: 26551.

KU KUMA KARANTA:Gwamnatin Yobe za ta mayar da kwale-kwalen Dufuna mai shekaru 8,000 zuwa cibiyar yawon buɗe ido

Malam Aliyu-Daura ya yabawa Gwamna Dikko Raɗɗa da kuma tsohon gwamnan jihar Aminu Masari wanda ya gada, a bisa rawar da suka taka wajen ganin Shema ya sauya sheƙa.

Don haka ya tabbatar wa tsohon gwamnan cewa za a yi masa adalci kamar kowane ɗan jam’iyya.

Shugaban ma’aikata na Raɗɗa, Jabiru Abdullahi-Tasuri, shi ne ya miƙa katin zama ɗan jam’iyya ga Shema a madadin gwamnan a jiya Alhamis a Dutsin-ma.

Continue Reading

Labarai

Fusatattun matasa sun lakaɗawa kwamishina duka a wajen zaɓen fidda gwani

Published

on

Banji Ajaka, kwamishinan lafiya na jihar Ondo, ya gamu da fushin matasa a jiya Asabar yayin da ake gudanar da zaɓen fidda gwani na gwamna na jam’iyyar APC mai mulki a jihar.

Daily Trust ta gano cewa Dakta Ajaka, wanda ke Mazaɓar Ugbo 3, a ƙaramar hukumar, ana zarginsa da ɓoye takardar sakamakon zaɓen.

Shaidu sun tabbatar da faruwar lamarin a wata tattaunawa da suka yi da manema labarai, inda suka yi zargin cewa fusatattaun matasan ‘ya’yan jam’iyyar APC ne da ke adawa da tsarin da aka bi wajen gudanar da zaɓen.

Ɗaya daga cikin waɗanda suka shaida lamarin, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya bayyana cewa rikicin ya faro ne lokacin da ‘yan ɗaya ɓangaren na jam’iyyar suka buƙaci ganin takardar sakamakon zaɓen na fidda gwani.

KU KUMA KARANTA:An yi jana’izar tsohon gwamnan Ondo, Rotimi Akeredolu

“Sun fusata ne suka buƙaci jami’in zaɓe ya ba su takardar sakamakon zaɓen sai kuwa ya ce ta na wajen Ajaka.

“Don haka suka yi masa duka a wurin, inda kuma garinsu ne. Jama’a sun fusata sosai da lamarin, inda rigimar ta ƙare a wajen.”

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, Dakta Ajaka ya ce an zarge shi ne da riƙe takardar sakamakon zaɓen.

Ya yi bayanin cewa a lokacin da yake ƙoƙarin bayyana kansa, ’yan daban sun auka masa inda suka yi masa mugun duka.

Continue Reading

GOCOP ACCREDITED MEMBER

You May Like