Birnin Almaty, birnin da ya shahara da yawan tsirrai na Tufafi a Kazakhstan

0
61

Almaty, birni mafi girma a Kazakhstan, ya shahara da fa’ida saboda yawan tsirrai na Tuffa masu daɗi a ƙasar. Sunan birnin ya samo asali ne daga ‘ya’yan itaciyar Tuffa.

Da yake a kudancin Kazakhstan, birnin Almaty ya kasance cibiyar hada-hadar kasuwanci da mahimmanci ga ‘yan kasuwa da ke tafiya a kan tsohuwar hanyar Silk, ya na kuma shaida yawan kasuwanci da haɗin guiwar al’adu tsakanin nahiyar Turai da Asiya.

A yau, kuma har yanzu ya na ɗaya daga cikin manyan cibiyoyin tattalin arziƙi, da kasuwanci da al’adu na ƙasar.

KU KUMA KARANTA:Ko kasan cewa ƙasar Tanzaniya ta fi kowace ƙasa yawan dabbobi a duniya?

Birnin Almaty, ya na tsakiyar sabuwar hanyar Silk, kuma ya na samar da damarmaki don bunƙasa yawon buɗe ido, da sabbin hanyoyin bunƙasa ƙirƙira da fasaha, da samun sabbin cibiyoyin saka hannun jari.

Hukumomin birnin na buri da kuma tsara shi domin zama babbar hanyar sufuri, dabaru da cibiyar yawon buɗe ido.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here