Ma’aikatan lafiyar Najeriya na barazanar shiga yajin aiki don goyon bayan ASUU

0
216

Ƙungiyar maaikatan lafiya a Najeriya ta yi barazanar shiga yajin aiki na sai abin da hali ya yi don nuna goyon baya ga kungiyar malaman jamio`i ASUU da sauran mayan makarantun kasar.

Ƙungiyar ta ce ba daidai ba ne a ce an bar makarantun kasar a rufe fiye da wata biyar.

Comrade Auwalu Yusuf Kiyawa, muƙaddashin babban magatarkarda na ƙungiyar ma’aikatan lafiya ta Najeriya, ya shaidawa BBC tuni suka sanar da gwamnati da ‘ya`yan ƙungiyar game da shirin yajin aikin.

Leave a Reply