Wasu ‘yan Nijar sun yi zanga-zangar neman ficewar sojojin Amurka daga ƙasar

0
33

Zanga-zangar wanda ta samu halartar shugabanin majalisar soja ta CNSP shi ne na farko da aka shirya domin nuna ƙin jinin dakarun Amurka dake da sansani a yankin Agadez.

Wasu dubban ‘yan jamhuriyar Nijar sun gudanar da gangamin a ranar Asabar a harabar majalissar dokokin ƙasar dake birnin Yamai da nufin matsa lamba ga sojojin Amurka su fice daga ƙasar, makwanni kusan 4 bayan da hukumomin ƙasar ta Nijar suka ba da sanarwar yanke hulɗar ayyukan soja da Amurka.

KU KUMA KARANTA:Wani harin bam ya kashe sojojin Nijar 6

Shugabar ƙungiyar mata ‘yan gwagwarmaya ta Nijar, Madam Fatima ta ce, sun fito gangamin ne domin nuna wa duniya irin ƙarfin da ‘yan ƙasar ke da shi, da kuma jaddada goyon bayan su ga jagororin mulkin sojin ƙasar bisa ƙudurin da suka ɗauka na umartar sojojin Amurka su fice daga ƙasar.

Ta ƙara da cewa, kamar yadda sojojin Faransa suka fice daga Nijar, lallai ne su ma sojojin Amurkan su hanzarta ficewa daga ƙasar, kuma ‘yan ƙasar Nijar na goyon bayan wannan mataki na gwamnatin CNSP.

Leave a Reply