Isra’ila ta fara shirin ko-ta-kwana domin tunkarar hare-haren Iran

0
86

Jiragen Iran marasa matuƙa sun nufi Isra’ila, in ji Press TV na ƙasar Iran mai yaɗa labarai da harshen Ingilishi, yayin da ya ambato majiyoyin Iran.

A jiya da rana shugaban Amurka Joe Biden ya katse bulaguronsa da yake yi a jihar Delaware zuwa fadar White House, domin tattaunawa da hukumar tsaro ta ƙasa a kan hare haren saman Iran kan Isra’ila, lamarin dake shirin ɗauke hankali a sa’o’i masu zuwa, a cewar White House a jiya Asabar.

Rukunin tsaron ƙasa yana bai wa shugaban ƙasa bayanai akai-akai a kan halin da ake ciki kana shugaban na tuntuɓar jami’an Isra’ila, haka zalika yake tuntuɓar ƙawayen Amurka, in ji kakakin hukumar tsaron ƙasa Adrienne Watson, yana faɗa a wata sanarwa.

KU KUMA KARANTA:Dole Chaina da Turkiyya su hana Iran kai harin ramuwar gayya a Isra’ila — Blinken

Tehran ta lashi takobin ɗaukar fansa kan harin da Isra’ila ta kai ta sama a harabar ofishin jakadancinta a Damacus, babban birnin Syria da ya kashe mutane 16 ciki har da wani babban kwamanda rundunar juyin juya hali na ƙasar dake zaune waje da wasu jami’ai 6.

A halin da ake ciki, Isra’ila tana zama cikin shirin ta kwana kana ta soke duk wasu harkokin karatu da na matasa.

Wata sanarwar ma’aikatar tsaron Amurka ta Pentagon ta ce sakataren tsaron Amurka Lloyd Austin ya yi magana da ministan tsaron Isra’ila Yoav Gallant a kan ɗaukar matakin gaggawa kan barazanar yankin.

Austin ya jaddada cikakken goyon bayan Amurka ga Isra’ila daga duk wani hari da Iran ko ƙawayenta za su kai mata.

Leave a Reply