Iran ta kai hari mafi muni kan Isra’ila

0
28

Daga Ibraheem El-Tafseer

Iran ta bayyana cewa ta ƙaddamar da hare-hare kan Isra’ila ta hanyar amfani makaman roka da kuma jirage marasa matuƙa.

Wata sanarwa daga Dakarun juyin-juya-hali na ƙasar Iran (IRGC) ta ce “an harba gwamman jirage marasa matuƙa da kuma makamai masu linzami zuwa cikin yankin ƙasar Isra’ila.

Dama an shiga fargaba kan yiwuwar ɓarkewar faɗa tsakanin Iran da Isra’ila tun bayan zargin da Isra’ilar da kai hari kan ofishin jakadancin Iran a Syria ranar ɗaya ga watan Afrilu.

Harin ya yi sanadiyyar kashe jami’an Dakarun juyin-juya-hali na Iran, waɗanda suka haɗa da janar-janar guda biyu da kuma wasu ‘yan kasar Syria shida.

KU KUMA KARANTA:Isra’ila ta fara shirin ko-ta-kwana domin tunkarar hare-haren Iran

Tun a wancan lokaci ne Iran ta yi gargaɗin cewa ‘Isra’ila za ta ɗanɗana kuɗarta’.

Sanarwar da Iran ta fitar ta ƙara da cewa harin na yammacin ranar Asabar martani ne kan “manyan laifukan da Isra’ila ta sha tafkawa” – ciki har da harin ranar ɗaya ga watan Afrilu.

Bayanin ya ce an yi wa wannan hare-hare da Iran ta ƙaddamar taken “Operation True Promise” a turance.

Sai dai sanarwar ba ta yi ƙarin haske kan yanayin harin ba, baya ga cewa ƙasar ta harba gwamman makamai zuwa cikin Isra’ila.

Kwamandan rundunar sojin Iran ɗin, ya ce ba su saɓa seti ko ɗaya ba, na harin da suka ƙaddamar kan Isra’ila.

Leave a Reply