Wani magidanci ya hallaka matarsa da dutsen guga a jihar Kano

0
98

Kotun majistre mai lamba 26 ta aike da wani magidanci Adamu Ibrahim gidan yari bisa zarginsa da hallaka matarsa ta hanyar buga mata dutsen guga a fuska.

Lamarin ya faru ne a garin Kwanar Ɗangora da ke ƙaramar hukumar Kiru a Jihar Kano.

Adamu ya bayyana cewar saɓani ne ya shiga tsakaninsa da matarsa dalilin wata mata da ta nuna ba ta son mu’amalarsa da ita.

KU KUMA KARANTA: Yadda mahauci ya kashe matarsa saboda wayar hannu a Adamawa

Sai dai ya ce ya yi ƙoƙarin fahimtar da ita, amma abin ya ci tura, inda ta ce babu ita babu zama da kishiya.

Daga nan ne a cewarsa ta kama shi da kokawa, kuma duk da ihun da yake yi ta ƙi rabuwa da shi, har ya aikata abinda ya aikata.

Leave a Reply