Labarin yana gefen ku!

Gwamnati ta yi wa ma’aikata da ’yan fansho ƙarin albashi

1

Gwamnatin Tarayya ta yi wa ma’aikatanta karin albashi da kashi 25% zuwa kashi 35%.

Kazalika gwamnatin ta yi wa ’yan fansho karin kashi 20% zuwa kashi 28% a kan albashinsu na yanzu.

Sanarwar da kakakin hukumar albashi ta kasa, Emmanuel Njoku, ya fitar ranar Talata, ta ce duk karin albashin da gwamnati ta yi zai fara aiki ne daga ranar 1 ga watan Janairu, 2024.

Ma’aikatan da aka yi wa ƙarin albashi sun hada da masu karbar albashi na bai-ɗaya, wato Consolidated.

KU KUMA KARANTA: Ƙungiyar ƙwadago ta buƙaci gwamnati ta biya ma’aikata 615,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi

Wannan karin albashi na zuwa ne a jajabirin bikin Ranar Ma’aikata ta Duniya ta bana.

Ƙungiyar ƙwadago ta Najeriya (NLC) dai ta daɗe tana neman a yi wa ma’aikata karin albashi, bisa la’akari da yadda abubuwan masarufi suka yi tashin gwauron zabo a ƙasar tun bayan da gwamnati ta sanar da janye tallafin mai a ranar 29 ga Mayu, 2023 da aka rantsar da Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu.

Ƙungiyar ma’aikatan jami’a ta  bayyana cewa mambobinta ba za su amince da mafi ƙarancin albashin da ya gaza Naira dubu 300 ba.

Kawo yanzu dai ƙungiyoyin ba su ce komai kan ƙarin albashin ba.

Leave A Reply

Your email address will not be published.