Sanata ‘Yar’adua ya tallafawa makarantar makarfi

0
100

Daga Idris Umar Zariya

Sanata Abdul’aziz Musa ‘Yar’adua, (Mutawallen Katsina) ya tallafawa makarantar makafi ta Katsina da kayan aiki.

Sanatan wanda Injiniya Surajo Yazeed Abukur PhD ya wakilta yayin gabatar da tallafin kayan rubutu da kayan aiki ga ɗaliban da Malaman makarantar ta makafi dake Katsina.

Injiniya Surajo Yazeed ya bayyana wannan matsayin somin taɓi ne wasu abubuwan alheri na nan tafe musamman ɓangaren ƙoƙarin Sanatan wajen tallafawa masu buƙata ta musamman.

Shi ma shugaban makarantar ya yi godiya a madadin malamai, iyayen yara, da ɗaliban makarantar ya yi fatan alheiri ga Sanatan bisa wannan kulawa da yake ba su.

Da yawan jama’a nayin fatan alheri.

Leave a Reply