Mutum fiye da 500 sun warke daga cutar sanƙarau a Yobe

0
103

An bayyana cewar ya zuwa yanzu aƙalla mutum 564 sun samu waraka daga cutar Sanƙarau da aka samu barkewar ta a Jihar Yobe.

An sanu ɓullar cutar karon farko a ranar 24 ga Disamba 2023, kuma mahukunta suka tabbatar da ita a ranar 26 ga Janairu na wannan shekara a Jihar Yobe.

Alƙaluman da mahukunta suka fitar sun nuna cewa, aƙalla marasa lafiya 564 daga cikin 636 da aka samu da kamuwa da cutar sanƙarau tun farko a jihar ta Yobe sun murmure.

Jami’in sa ido da sanar da cututtuka na hukumar kula da lafiya a matakin farko, Haruna Umar ne ya bayyana hakan a wata hira da manema labarai a Damaturu.

Malam Umar ya ƙara da cewar, an samu rahoton mutuwar mutane 22, yayin da marasa lafiya 564 suka warke da kuma ragowar mutum 50 da ake ci gaba da kulawa da su a cibiyoyin da keɓe wa masu ɗauke da wannan cuta.

KU KUMA KARANTA: Ɓullar cutar sanƙarau a Yobe, ɗalibai sama da 20 sun mutu

Har ila yau, ya ƙara da cewa, mutum 636 da aka samu da cutar sun fito ne daga kananan hukumomi shida da suka hada da Machina, Nangere, Fika, Fune, Potiskum da Gujba.

Jami’in kiwon lafiyar ya tabbatar da cewa gwamnati ta ɗauki matakan gaggawa ne wajen  dakile yaduwar cutar a jihar tun farko wadda kuma Allah Ya ba su nasara ta daina bazuwa a sauran sassan Jihar.

“Gwamnati ta kafa cibiyoyin jinya a kananan hukumomin da abin ya shafa, ciki har da sansanonin keɓewa na wucin gadi a wasu makarantun sakandare da lamarin ya fi tsamari don hana bazuwar ta.

“Haka kuma, gwamnati ta ɗauki ma’aikatan wucin gadi 18, ciki har da likitoci biyu a cibiyoyin da aka keɓe da sauran matakan,” in ji Umar.

Leave a Reply