Yadda za a magance fitowar gemu a fuskar mace

0
139

Gemu ga ’ya mace  na ɗaya daga cikin abubuwan da ke bata fuska da kuma kwalliyarta.

Domin yana ɓata mata adonta. Sai a ga duk hoda da fandesho da aka sa ba sa kawar da hakan. Don haka ne a yau na kawo muku hanya mafi sauƙi wadda za a bi domin magance fitar gemu a fuskar ‘ya mace.

· Za a iya rabuwa da gemun idan an yi amfani da man cire gashi a jiki kamar (hair remobal cream). Sannan a samu auduga a jika da ruwa a goge wajen da aka cire gemun.

·Kurkum na ƙara taimakawa bayan an cire gashin wajen sai a shafa shi domin kada ya nuna alamar cire gashi daga inda gemun ya fito.

KU KUMA KARANTA: Na fara sana’a ne don na dogara da kaina – Zainab Aqeela Katsina

·Yana da kyau a kwaɓa kurkum da zuma sannan a shafa a fuska kafin a kwanta barci. Yin haka na kare fuska daga sake fitowar wani gashin.

·Amfani da nikakken karas da nono ko madara na ƙara gyara inda gashin ya fito.

Domin rabuwa da irin wannan matsalar ta hanyar sauki, shawara ita ce kada a yi amfani da wani man kanti ko wani sabulu.

A yi amfani da waɗannan bayanan da na bayar don samun biyan buƙata.

Leave a Reply