Ƙaruwar cutar kwalara na da alaƙa da sauyin yanayi – WHO

0
121

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta sanar da cewa cutar amai da gudawa ta kwalara na da alaƙa mai ƙarfi da matsalolin sauyin yanayi.

Dakta Kate O’Brien wadda ita ce daraktar rigakafi ta hukumar, ta bayyana haka ne a wani taron manema labarai.

“Ina ganin ya kamata mu san cewa ɓarkewar cutar kwalara da ake fama da ita na da alaƙa da sauyin yanayi, kuma mun ankarar dangane da kwalara,” in ji O’Brien.

“Ba wai batun rigakafi ne kaɗai ba, a gaskiya ba ita ce kaɗai hanyar farko ta kariya daga kwalara ba. Kwalara cuta ce da ke da alaƙa da tsaftar ruwa da tsaftar muhalli. Kuma rigakafi hanya ce ta kiyaye cuta idan akwai ta.”

KU KUMA KARANTA: WHO ta taimaka wajen kwashe marasa lafiya 14 daga Asibitin Nasser da ke Gaza da aka yi wa ƙawanya

Haka kuma O’Brien ta bayyana cewa a halin yanzu duniya na shirin fuskantar ɓarkewar cutar ƙyanda.

“Sakamakon ɓarkewar cututtuka da ake samu, sauyin yanayi da ƙaruwar jama’a da matsalolin ayyukan jin ƙai, batun kiyaye cututtuka ta hanyar rigakafi ba zai zama lamari mai muhimmanci ba a yanzu,” in ji ta.

Leave a Reply