Me ke jawo wa likitoci ke fice wa daga Najeriya?

0
76

Hukumomi sun ce tsakanin likitocin 15,000 zuwa 16,000 ne suka yi ƙaura a cikin shekaru biyar da suka gabata. Hakan ya bar ƙasar da ta fi fice a Afirka da likitoci 55,000 kacal ga al’umma miliyan 220.

Ma’aikatar lafiya ta Najeriya ta ce dubban likitoci da ma’aikatan jinya na barin Najeriya duk shekara domin samun fiyayyun damarmaki a ƙasashen waje. Daga cikin abubuwan da ke sa su ƙaura sun haɗa da hauhawar farashin kayayyaki, ƙarancin albashi da kuma tsarin kiwon lafiya da komai ya mai yawa.

Yawancinsu su na tattare ne a manyan biranen ƙasar, amma ga sauran ƙasar, akwai likitoci biyu kacal ga kowane mutum dubu 10.

KU KUMA KARANTA:An kama likita bisa zargin sace jariri a Abuja

Kamfanin dillancin labaran Faransa AFP ya bayar da rahoton cewa, likitoci a Najeriya da ma wasu asibitoci masu zaman kansu suna samun dala 2,000 zuwa dala 4,000 a duk shekara, wato kusan dala 200 a wata.

Gwamnati na duba yiwuwar ƙarin albashin ma’aikatan jinya. Majalisar tana nazarin wani ƙudirin doka da zai buƙaci waɗanda suka kammala karatun likitanci su yi aiki na tsawon shekaru biyar a Najeriya kafin su samu cikakken lasisin yin aiki. Kuma wata sabuwar doka ta buƙaci ma’aikatan jinya su yi aiki aƙalla na tsawon shekaru biyu a Najeriya kafin su bar ƙasar.

Leave a Reply