An kama likita bisa zargin sace jariri a Abuja

0
80

’Yan sanda na gudanar da bincike a kan ɓacewar wani jariri, sa’o’i ƙalilan bayan haihuwarsa a wani asibiti mai suna Trendy Hospital Clinic and Maternity da ke Unguwar Dutse Makaranta, a Ƙaramar Hukumar Bwari a Abuja.

An kama likitan ne tare da rufe asibitin nasa a ranar Lahadin da ta gabata, bayan bore daga mazauna yankin a kan lamarin, wanda ake zargin ba shi ne karo na farko ba.

Mahaifiyar jaririn mai suna Favour Idowu mai shekara 17, an garzaya da ita wani asibiti da ke yankin, inda take samun kulawa.

A zantawarta da Aminiya, ta ce ta ziyarci likitan a ranar Larabar makon jiya a kan matsalar murdar ciki da ya addabe ta.

Ta ce, “Ya ba ni kwayar magani da ya umarce ni da na saka a ƙarƙashin harshena, sannan ya cusa min wani a cikin al’aurata.

“Bayan wani lokaci sai na fara jin nakuɗa da ya ci gaba da murɗewar ciki har zuwa ranar Asabar lokacin da na haihu.

KU KUMA KARANTA: Baƙuwa ta sace jariri awa 3 da haihuwarsa a asibiti

“Ya bugi jikin yaron inda ya yi kuka, ba ajima ba sai na suma, daga baya bayan na farfaɗo sai na ga jariri a kusa da ni.

“Bayan wani lokaci sai wasu mata biyu suka fita da yaron. Likitan ya shaida mini cewa za su yi masa riga-kafi ne, shi ne ganin ƙarshe da na yi wa yaron, bayan na farka ne sai na gan ni a wannan asibitin na yanzu,” inji Favour.

Ta kuma musanta zargin da ake yi kan akwai yarjejeniyar likitan zai ba ta wani kudi, kuma kasancewa an fuskanci akasi a lamarin ne, maganar ta kai ga ’yan sanda.

Ta yi ƙorafin cewa, wanda ke da alhakin yi mata cikin, ya musanta lamarin tun a watannin farko na cikin.

Wani ɗan uwan mahaifiyar jaririn mai suna Samuel Idowu, ya ce, sun shigar da ƙara a gaban ’yan sanda a kan lamarin sannan daga bisani aka samu nasarar kama likitan.

Ya ce, ’yar uwar tasa ta dawo hayyacinta ne bayan ta shafe kwana biyu a sabon asibitin da a kai ta, inda take ci gaba da zaman jinya har zuwa shekaran jiya Laraba.

Wani mai makwbtaka da asibitin da ya nemi a sakaya sunansa ya ce, kamar mako uku gabanin faruwar lamarin, an ji wata mata tana rigima da likitan kan alƙawarin yaro da ya yi mata ba tare da cikawa ba.

Haka kuma wata majiya ta ce, an kama wata mazauniyar yankin Arab road da ke garin Kubwa a ranar Litinin da ta gabata a kan wani al’amari da ke da nasaba da kama likitan.

Babban jami’in ‘yan sanda na Dutsen-Alhaji, CSP Paul Danladi ya tabbatar da faruwan lamarin.

Ya ce, an kama waɗanda ake zargin, sannan ana neman wani saurayin uwar jaririn mai suna Joseph da ake zargi da kai ta wajen likitan sannan ya karɓi naira dubu ɗari huɗu ya gudu.

Ya ce, an miƙa ƙarar zuwa Rundunar ‘yan sanda ta Abuja don ci gaba da gudanar da bincike a can, kasancewar iyalan da jaririn ke hannunsu sun shigar da ƙara kan lamarin a can.

Leave a Reply