Bello Turji ya fara ƙaddamar da hari akan ‘yan bindigan Zamfara, bayan Gwamna Matawalle ya masa afuwa

0
500

Daga Saleh INUWA Kano

Bello Turji, wanda Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara, ya yi wa afuwa, a yanzu haka yana ƙaddamar da farmaki kan ‘yan taadda a yankunan da suka mamaye domin tabbatar da cewa zaman lafiya da kwanciyar hankali ya dawo jihar.

Mataimakin gwamnan jihar Zamfara Sanata Hassan Nasiha ne ya bayyana hakan a yayin wani taro kan harkokin tsaro da kungiyar dalibai da wata jami’ar Madina ta shirya a Gusau babban birnin jihar.

Hassan ya yabawa Turji bisa matakin da ya dauka na ajiye ayyukan fashi da makami, da kuma matakin taimakawa wajen samar da zaman lafiya a ƙananan hukumomi uku da ke kan gaba wajen fuskantar hare-hare yan bindiga a jihar Zamfara.

A cewar mataimakin gwamnan, tun makwanni biyar da suka gabata ba a samu wata arangama tsakanin Fulani da Hausawa a kananan hukumomin Birnin Magaji, Shinkafi da Zurmi na jihar ba, sakamakon tattaunawar sulhun da aka yi tsakanin bangarorin biyu da ke rikici da juna a jihar.

Gidan talibijin na Channels ya ruwaito mataimakin gwamnan na cewa, kwamitin da Gwamna Bello Matawalle ya jagoranta ya gudanar da taron zaman lafiya da sansanonin yan bindiga tara a gundumar Magami da Masarautar Dansadau na ƙananan hukumomin Gusau da Maru na jihar domin su daina kai hare-hare ga mutanen da ba su ji ba ba su gani ba.

Ya ci gaba da cewa, Turji wanda Gwamna Bello Matawalle ya yi wa afuwa, a yanzu haka yana kaddamar da farmaki kan yan taadda a yankunan da suka mamaye domin tabbatar da cewa zaman lafiya da kwanciyar hankali ya dawo jihar.

Leave a Reply