Gwamna Mai Mala Buni ya samarwa ‘ya’yan marigayi Sheikh Baba Goni Aisami aikin yi

0
342

Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya ba da umarnin ɗaukar aiki kai tsaye ga ‘ya’yan marigayi malamin addinin Islama, Sheikh Goni Aisami, wadanda aka kashe a ranar Juma’ar da ta gabata a kusa da Gashua.

Gwamna Buni ya bayar da umarnin ne a yau a lokacin da ‘yan uwa suka ziyarce shi domin nuna godiyar su ga mai girma Gwamna Mai Mala Buni, bisa kulawar sa ga iyalan.

Mai magana da yawun Gwamna Mamman Mohammed, shi ya sanar da hakan a hukumance.

Gwamna Buni ya tabbatar da cewa gwamnati za ta tabbatar da gudanar da bincike kan lamarin mutuwar malamin.

Ya kuma ba da tabbacin gwamnati za ta ci gaba da tallafa wa ‘yan uwan saboda Babban rashi da akayi.

Malam Ibrahim Aisami, wanda ya yi magana a madadin ‘yan uwa, ya nuna jin daɗinsa da sakon ta’aziyya da ziyarar da wata babbar tawagar gwamnati ta kai domin jajantawa iyalan.

Ya ce aikin zai rage wa iyalansu wahala sakamakon rasuwar malamin.

A ranar Juma’ar da ta gabata ne wasu da ake zargin sojoji ne su biyu, suka kashe Shiek Aisami.

A halin da ake ciki dai, ‘yan sanda sun kama waɗanda ake zargin, yayin da rundunar sojin ta sanar da cewa ta fara gudanar da bincike a kan lamarin domin bayyana cikakken bayani kuma duk wanda aka samu yana so zai fuskanci shari’a.

Rahoton: Ibrahim Bulama Lamba – S.A Social Media.
23 August, 2022.

Leave a Reply