Abu biyar daya kamata ku sani game da Ademola Adeleke

0
291

Daga Fatima Gimba, Abuja

Da safiyar Lahadi ne hukumar INEC a Najeriya ta sanar da Sanata Ademola Adeleke na Jam’iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan Jihar Osun.

Babban baturen zaben Jihar, Farfesa Oluwatoyin Ogundipe, ya ce Sanata Adeleke ya samu kuri’a 403,371.

Sai kuma gwamnan jihar na yanzu wato Adegboyega Oyetola na jam’iyyar APC ya zo na biyu da kuri’a 375,027.

READ ALSO: Adeleke Na Jam’iyyar PDP Ya Kayar Da Gwamnan Osun Mai Ci Oyetola Na Jam’iyyar APC

Ko a 2018, sai da aka kara tsakanin Oyetola da Adeleke, inda zaɓen ya zama wanda bai kammalu ba, bayan INEC ta shirya zaɓe zagaye na biyu sai Oyetola ya samu nasara.

Adeleke ya yi fice matuƙa sakamakon yadda ya iya rawa kuma ana ganin bidiyonsa a shafukan sada zumunta na yadda yake dagewa wajen rawa musamman idan ya je bukukuwa.

Ga wasu abubuwan suka kamata ku sani game da Ademola Adeleke:

• Ademola Adeleke ƙane ne ga gwamnan farar hula na farko na Jihar Osun, Marigayi Sanata Isiaka Adetunji Adeleke.

• An zaɓi Ademola a matsayin sanata mai wakiltar Yammacin Osun a 2017 domin ɗorawa kan wa’adin ɗan uwansa da ya rasu. A baya shi ba ɗan siyasa ba ne amma masu sharhi kan siyasa sun ce jama’a da dama sun zaɓe shi ne saboda yayansa yana da kyakkyawan nufi ga jihar.

• Mahaifinsa ya taɓa sanata a Najeriya sai kuma mahaifiyarsa malamar Addinin Kirista ce.

• Ademola, kawu ne ga shahararren mawaƙin nan na Najeriya Davido. Mahaifin Davido, Adedeji Adeleke yaya ne ga Ademola.

• Ya kammala digirinsa a fannin kimiyyar nazarin laifuka a 2021 daga kwalejin Atlanta Metropolitan State College da ke Amurka bayan tirka-tirkar da aka yi ta yi game da tarkardun karatunsa inda har aka kai shi kotu.

Leave a Reply