Ba mu sami umarnin kotu kan dakatar da Ganduje ba – APC

0
207

Hedikwatar Jam’iyyar APC ta Ƙasa ta ce ba ta da masaniyar umarnin kotu da ke dakatar da shugaban jam’iyyar, Abdullahi Ganduje.

Mai ba jam’iyyar shawara ta fuskar shari’a, Farfesa Abdulkarim Kana, ya ce ba su sami umarnin Babbar Kotun Jihar Kano kan shugaban jam’iyyar, wanda shugabannin mazabarsa suka dakatar ba.

Ya bayyana wa manema labarai a hedikwatar jam’iyyar da ke Abuja ranar Laraba cewa, “mun ji dai ana magana kan umarnin kotun, amma dai bai zo hannunmu ba.

KU KUMA KARANTA: An kori Abdullahi Umar Ganduje daga jam’iyyar APC a mazaɓarsa

“Waɗanda suka dakatar da shi ba mambobin jam’iyyar APC ba ne, kuma ba sa cikin jagororinta ba ne a Jihar Kano. Ba mu san su ba,” in ji Farfesa Kana.

Ya ci gaba da cewa, “Shugabancin jam’iyyarmu ya riga ya rubuta wa shugaban ’yan sanda takardar korafi kan lamarin.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here