Adeleke Na Jam’iyyar PDP Ya Kayar Da Gwamnan Osun Mai Ci Oyetola Na Jam’iyyar APC

1
184

Gwamnan jihar Osun, Gboyega Oyetola, ya sha kaye a zaɓensa na sake tsayawa takara karo na biyu a hannun ɗan takarar jam’iyyar adawa ta PDP, Sanata Ademola Adeleke.

A baya mun samu rahoto cewa, Adeleke ya lashe ƙananan hukumomi 17 daga cikin 30 na jihar yayin da gwamna mai ci kuma dan takarar jam’iyyar APC, Gboyega Oyetola, ya lashe sauran kananan hukumomi 13.

Yayin da Adeleke ya samu ƙuri’u 403,371 a zaben gwamnan jihar Osun da aka gudanar a ranar Asabar 16 ga Yuli, 2022, Gwamna Oyetola ya samu kuri’u 375,027.

Da yake sanar da sakamakon karshe a safiyar Lahadi, babban jami’in zabe na INEC, Farfesa Oluwatoyin Temitayo Ogundipe, wanda shi ne mataimakin shugaban jami’ar Legas (UNILAG), ya ayyana Ademola a matsayin wanda aka zaba saboda ya samu mafi yawan ƙuri’u.

1 COMMENT

Leave a Reply