Za’a rufe kasuwar canji a Abuja, har sai abin da hali ya yi

0
56

Daga Ibraheem El-Tafseer

Ƙungiyar ‘yan kasuwar canji ta Abuja ta ce daga ranar Alhamis za ta rufe kasuwar canji har sai abin da hali ya yi sakamakon tsadar dala da ake fama da ita a Najeriya.

Shugaban ƙungiyar, Alhaji Abdullahi Dauran shi ne ya sanar da hakan a wani taron manema labarai a Abuja.

Darajar takardar kuɗin Najeriya, wato Naira ta yi faɗuwar da ba ta taɓa yi ba cikin gomman shekaru na tarihin ƙasar.

A kasuwar canji, a ranar Talata, an yi musayar naira kan kowace dala a kan Naira dubu 1,520 yayin da a hukumance ake sayar da dala kan Naira ɗari 892 da Naira ɗari 910.

KU KUMA KARANTA: Bashin da Najeriya ta ciwo ya ƙaru zuwa tiriliyan N89.3

Ƙungiyar ‘yan canji ta alaƙanta tashin farashin dalar da ayyukan kamfanin da ke hada-hadar kuɗaɗe ta Intanet irin na Crypto da ake ƙira Binance

Hakan ne ya sa ƙungiyar ta yi ƙira ga gwamnatin Najeriya da ta hana ‘yan Najeriya hulɗa da kamfanin na Binance, idan dai har ana son karyewar farashin dalar.

Leave a Reply