Ministar ma’aikatar kasuwanci ta Burtaniya ta iso Najeriya domin ziyarar kwanaki uku

0
37

Ministar kasuwanci ta Burtaniya, Kemi Badenoch ta iso Najeriya domin fara ziyarar aiki na kwanaki uku, da nufin zurfafa haɗin gwiwa tsakanin Burtaniya da Najeriya.

Bayan ziyarar tsohon sakataren harkokin wajen Burtiniya a watan Agustan shekarar 2023, da kuma tattaunawar tsaro tsakanin Najeriya da Burtaniya a makon jiya, ziyarar minista Badenoch za ta ɗora akan ƙoƙarin da ƙasashen biyu ke yi na bunƙasa hulɗar kasuwanci da kuma buɗe sabbin hanyoyin zuba jari.

A cewar wata sanarwa da ofishin jakadancin Burtaniya a Najeriya ta fitar, a yayin da take ƙasar, Minista Kemi Badenoch da jakadiyar Firai Minista ta musamman a fannin kasuwanci a Najeriya, Helen Grant, za su gana da gwamnatin tarayyar Najeriya, gwamnonin jihohi, da kuma shugabannin ‘yan kasuwa da masu zuba jari na Burtaniya da Najeriya.

KU KUMA KARANTA:Gwamnatin Kano ta rufe rumbunan masu ɓoye abinci 5

Ta hanyar waɗannan tarurrukan, ministar za ta duba halin da ake ciki da kuma damar zuba jari da harkokin kasuwanci daga ayyukan ilimi zuwa ga ayyukan more rayuwa da makamashi, da nufin samar da dubban ayyuka.

Da ya ke tsokaci kan ziyarar Badenoch Najeriya, shugaban ofishin jakadancin Burtaniya a Najeriya, Dokta Richard Montgomery ya ce, “Najeriya na ɗaya daga cikin manyan ƙasashen abokan hulɗar Burtaniya a Afirka. Burtaniya ta himmatu wajen taimaka wa Najeriya samun damar saka hannun jari, duk da nufin samar da ayyukan yi a ƙasashen biyu.”

Leave a Reply