Matatar mai ta Ɗangote ta soma sayar da fetur a Najeriya

0
118

Matatar mai ta Ɗangote da ke Najeriya ta fara sayar da fetur a ƙasar a ranar Talata, in ji ƙungiyar tallatawa da sayar da mai ta kamfanin.

Wannan babban matakin tsayawa da ƙafafu ga Najeriya wajen biyan buƙatar makamashi da take da ita.

Mutumin da ya fi kowa kuɗi a Afirka Aliko Ɗangote ne ya gina matatar man, mafi girma a nahiyar a gaɓar tekun Legas kan dala biliyan 20, kuma an kammala aikin bayan tsaiko na shekaru da dama da aka samu.

Matatar na iya tace gangar ɗanyen mai 650,000 kowace rana, kuma idan ta fara aiki ɗari bisa ɗari za ta zama mafi girma a Afirka da Turai.

KU KUMA KARANTA: Ɗalibi ya lashe N5 miliyan a tallan siminti na Dangote

Daraktan rukunan kamfanonin Dangote Devakumar Edwin ya tabbatar da cewa sun fara sayar da man dizel da man jiragen sama a ƙasar.

Edwin ya shaida wa Reuters cewa “Muna da isasshen mai. Ana jigilar man ta ruwa da ƙasa. Jiragen ruwa na bin layi ɗaya bayan ɗaya don ɗiban dizel da man jiragen sama.”

“Jiragen ruwa na ɗaukar lita miliyan 26, amma muna ƙoƙarin ganin an kawo jiragen da ke ɗaukar lita miliyan 37 don sauƙaƙa ayyukan.”

Ƙungiyar masu sayar da man ta amince kan sayar da kowacce litar dizel naira 1,225 bayan ƙulla yarjejeniya kan tsayar da farashi, in ji Abubakar Maigandi, Shugaban ƙungiyar Masu Sayar da Man Fetur Mai Zaman Kanta a Nijeriya.

Mambobin ƙungiyar na da gidajen mai kimanin 150,000 a faɗin Najeriya, in ji Maigandi.

Matatar mai ta Dangote na so ta kawo ƙarshen dogaro ga man da ake shigowa da shi daga ƙasashen waje da Najeriya ke yi.

Najeriya ce ƙasar da ta kowace yawan jama’a a Afirka, kuma tana kan gaba a tsakanin ƙasashen da ke fitar da albarkatun mai, amma tana sayo mai daga waje saboda ba ta da matatu.

Leave a Reply