NNPC ya sa matatar mai ta Fatakwal a kasuwa

0
81

Kamfanin mai na Ƙasa NNPCL ya tallata matatar mai ta garin Fatakwal da ta fara aiki ga ‘yan kasuwa masu zaman kansu waɗanda za su tafiyar da ita yadda ya dace.

Ana iya tuna cewa Gwamnatin Tarayya ta ce matatar za ta fara aiki gadan-gadan cikin watanni huɗun farkon wannan shekara.

A halin yanzu dai, ana sa ran matatar za ta fara da tace ganga dubu 60 a kowacce rana kafin daga bisani a fara tace ganga dubu 210 kowacce rana.

NNPCL a cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai, ya ce akwai buƙatar bai wa ‘yan kasuwa masu sha’awa damar gwada basirarsu wajen tafiyar da matatar don tabbatar da zamanta da kafafuwanta ba tare da samun wata matsala ba.

Sai dai kuma kamfanin ya ce duk ɗan kasuwar da ke buƙatar karɓar wannan matata sai ya nuna shaidar samun ribar aƙalla dala biliyan biyu tun daga shekarar 2019 a matsayin shaidar cewa shi ɗan kasuwa ne cikakke.

KU KUMA KARANTA: Matatar fetur ɗin Ɗangote ta fara samar da dizel da man jirgin sama

NNPCL ya ce a ranar 4 ga watan Janairu zai kammala gwaje-gwaje a matatar man ta Fatakwal, abinda ke nufin a yanzu fara aiki ne kawai ya rage.

Matatar man ta Fatakwal da aka rufe shekaru biyar da suka gabata na daga cikin matatun mai na gwamnati da aka shafe shekaru ana tafka muhawara a kansu, amma gwamnatin Najeriya na kokarin farfaɗo da su domin kawo ƙarshen dogaron da ƙasar ke yi kan kayayyakin da aka tace daga ƙasashen waje.

Ana dai ganin nuna halin ko in kula na gwamnatocin baya ne ya kashe manyan matatun biyu da ƙasar ke da su, yayin da siyasa ta dabaibaye gyaran su, duk da alƙawarin yin hakan da kowacce gwamnati ke yi a lokutan yaƙin neman zaɓe.

Leave a Reply