Yadda Aikin Watsa Labarai Ya Sauya Daga Shekara Ta 2000 Zuwa Yau

0
354

Daga; Musa Muhd Kutama, Kalaba.

AIKIN watsa labarai aiki ne Mai matukar mahimmancin da kwarjini, aiki ne wanda ke ilmantar da Jama’a, Nishadantar dasu da Kuma wayar musu da kai.

Tagomashin da aikin yake dashi ne da mahimmancin sa ya sanya ya samo asali tun daga zamani shekaru sama da dubu daya da wasu da’irai.

Alal misali, a Najeriya kowa al’umma da yadda take isar da sakon ta ga Jama’ar ta. A Arewacin Najeriya anyi amfani da Maishela wanda idan dare yayi kowa ya natsa yake bin kwararo-kwararo, da kowane lungu na unguwa yana shela yana cewa “Ya ku jama’a sarki ya gaisheku ya kuma ya gaisheku, bayan haka Sai ya isar da Umarnin sarki na Hani ne ko ma na Umarni ne.

A wasu yankunan kuma ana yin amfani ne da karattawa ana kadawa ko kuma Kuge, da nufin isar da labari ko Umarnin hukuma, Kafin daga bisani a samu Rediyo da Talbijin da Jaridu wajen isar da sako ga Al’umma .

A lokacin da aka kafa gidajen yada labaru a Najeriya a wancan lokaci sama da shekara goma na wancan lokaci ma’aikacin Jarida na yin amfani ne da Hanyoyi biyu wajen aikewa da labaransu kafar yada labaran da suke aiki kamar yadda Wani dan jarida da ya yi aiki da kayan aiki irin na ada da kuma yanzu wato Malam Naziru Abubakar yake cewa a sauyin da aka samu Zamanin.

Ya ce “Lokacin nan ai muna aikawa da labaran mu ta hanyoyi uku ne, na farko akwai wata na’ura da muke aikewa sakon karta kwana mai Suna Fax an makala ta ne da tarho zaka Kira layin ofishin ku can ka akwai mai karbar sakon shi kuma idan ya karba zai Kaiwa editan labari, ta haka muke aikewa da labari sannan akwai motocin dake kawo Jaridu mukan rubuta mu ajiye da zarar ankawo Jarida sai aba Direba ya tafi dasu idan ba labarin wanda zaiyi kwantai bane, mukan aika shi ta gidan waya.”- Inji shi

Sauyin Zamani.

Abbunakar ya ci gaba da cewa “Yanzu zamani ya sauya tun daga shekara ta 2000, zuwa wannan lokaci an daina amfani da na’urar Fax saboda zuwan yanar gizo sai aka rika aikawa da labarai ta yanar Gizo wato email lamarin da ake Gani ya saukaka aikin. ” 

Shi kuwa Francis Mike ma’aikacin Radiyo ne da ya shafe shekara 35 yana aiki kafin ya yi ritaya, ya shaida irin yadda rahoton radiyo yake da cin lokaci ta gajiyar da mutum wanda Idan za a aika rahoto Sai anje gaban waya an zauna an dinga Kiran waya kafin ka su layin idan akwai xinkosa ma ragowar Abokan aiki dake aika rahoton su.

Ya ce “wani lokaci kuma hanyar sadarwar idan akwai cinkosa, haka zaka hakura har sai an samu daidaito idan ma ka samu kafin aika muryar mutum biyu da kayi Hira dasu kake so muryar su ta fito cikin rahoton, inda sai ka ta tari’ar muryar mutumin tunda rikoda ce Mai zare sai ka kara rikodar jikin tarhon ka kunna can kuma Inda ake karbar rahoton akwai wata katuwar rikoda Mai zare yana jujjuyawa yana nadan sakon da ake aikowa.”

Ya kara da cewa “aiki ne jazur amma yanzu an samu saukin hanyar aikewa da rahoto musamman sabuwar fasahar zamani yanzu an samu rikodoji na zamani wanda zaka iya sauke muryar ta manhaja, a tace labarin sannan a aika yanzu wanda wayar salula zata iya yin komai yanzu.”

Imam sha’aibu, wani Dan Jarida ne da ya yi  bayani a kan kubalen da aikin Jarida ke fama dashi da Kuma sauyin akalar bayar da labaru yake inda ya kara bayani yadda aikin Jarida yake wancan lokaci da Kuma yanzu.

“To aikin Jarida kamar yadda aka sani, Dan Jarida idan yaje ya dauko rahoto ko labari zai dauko ne da Biro da Takarda yana takaice rubutun wato short hand idan ya dawo sai ya buda shi ya rubuta labarin a kaiwa edita shi ma ya duba A
ayi gyare-gyaren da za a yi har aka zo aka kai lokacin da ake yin amfani da Keken rubutun wato type-writer, kamin daga nan aka koma yin amfani da kwamfuta.”

“Anan zai rubuta labarin ya tace ya yi amfani da flash ya ciro ya aika ta hanyar intanet Bama flash na lokacin ana amfani da wani abu waishi Disket idan kuma Disket ya samu matsala shi ke nan Babu Jarida daga nan zamani yazo aka samu flash drive ta haka ake aikin na aikawa da labaran. “

Ya ci gaba da cewa anyi amfani da Telex Shi ma anyi amfani dashi lokacin ma ai ba a maganar email nata bunkasa ba, amma yanzu Duniya ta sauya yanzu mutum ma yana kwance a daki ma zai iya aika labarin ka bama sai taje ofis ba domin a yanzu duk yan jaridar wannan lokacin idan ka tambayesu fax machine basu ma sani ba sai Yan jaridun da suka shafe sama da shekara 20 Suna aikin ne kadai zasu san shi.

“Yanzu komai yazo cikin sauki zaka dauki labarai ka aika ba kamar ada da sai kayi wata da watanni naka ga ma editan ka ba, amma yanzu wayar Hannu zata iya yi maka komai ka dauki bidiyon ko odiyo ka tura komai cikin sauki kuma a samu biyan bukata “

Acewarsa, ra fuskar yadda kayan aiki na zamani ke shafar aikin jarida, Imam sha’aibu ya kara da cewa ” kafafen zamani suna baiwa ‘yan jaridu kalubale sosai musamman a zamanance na Kafafen sada zumunta na soshiyal midiya da aka samu zamanin ya kawo.

Babban Kalubale ga ‘yan Jarida yanzu shi ne na kafafen sada zumunta don yanzu kowa ya Zama dan Jarida wanda shi ne muke cewa ‘yellow Journalism ‘ yadda idan mutum yana da Babbar waya, da abu ya faru sai ya dauka ya tura shi ma a dole ya zama dan Jarida inda wani lokacin a labaran zaka samu an yada labaran bogi.

To amma yanzu an samu kwararrun ‘yan Jaridu da suke iya tantance hoto ko bidiyon na bogi da aka yada hoton ko daukar murya. Hakazalika idan mutum ya zama kwararre zai iya ganewa idan yaga na bogi domin abubuwa da zai dudduba ya iya ganewa akwai manhaja da ake zaton ana amfani da ita wacce zata nuna wannan abu na bogi ne.

Leave a Reply