Matasan Jihar Kano Suna Amfana Da Gwamnatin Ganduje – Inji Mustapha Coach

0
373

Daga; Jabiru A Hassan, Kano.

JAGORAN matasan Kano ta arewa Kwamared Mustapha Umar Tallo Gwarzo wanda aka fi sani da “Mustapha Coach” ya bayyana gwamnan Jihar Kano Dokta Abdullahi Umar Ganduje a matsayin gatan matasan Jihar.

Ya yi wannan tsokaci ne a zantawar sa da wakilin mu a Gwarzo, inda ya nunar da cewa “mai girma gwamna Dokta Abdullahi Umar Ganduje shugaba ne nagari wanda kuma yake kokarin kyautata rayuwar matasan jihar kano wanda hakan ya sanya a duk fadin kasar nan babu jihar da matasa ke amfanar gwamnati kamar jihar Kano.”

Kwamared Mustapha Coach ya Kuma bayyana cewa ko shakka babu gwamnati Ganduje ta cancanci a yaba mata saboda bullo da hanyoyi da take yi domin inganta rayuwar matasa da a fadin jihar ta hanyar basu horo da tallafin kama sana’oi na dogaro dakai kamar yadda ake gani a yau.

Yace baiwa matasa damar samun hanyoyi na dogaro dakai ya taimaka wajen wanzuwar zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar duk da irin dumbin aiyukan alheri na raya kasa da gwamnati keyi bisa la’akari da bukatun al’umar kowane bangare dake kananan hukumomi 44 da ake dasu a jihar ta Kano.

Jagoran matasan ya kuma ja hankalin matasan jihar Kano da su ci gaba da goyon bayan gwamnatin ta Ganduje treda kasancewa cikin bin doka da son zaman lafiya kamar yadda aka sansu tun da aka fara hawa kan tafarkin dimokuradiyya a wannan kasa tamu.

Haka Kuma yayi fatan alheri ga gwamna Ganduje da daukacin wadanda suke da madafun iko bisa yadda aka hada hannu ana aikin ciyar da jihar Kano gaba, tareda jaddada cewa zai ci gaba da kokarin da yake yi wajen kara hada kawunan matasan jihar ta kano domin rabauta daga kyawawan manufofin gwamnati.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here