Farfesa Hafsat Abdullahi Umar Ganduje: Jagorar Taimakon Al’umma

0
483

Daga; Jabiru Hassan, Kano.

A DUK lokacin da aka yi maganar taimakon al’umma, nakan bada misali da mai girma Uwar-gidan Gwamnan Jihar Kano watau Farfesa Hafsat Abdullahi Umar Ganduje wadda kuma muke kira (Goggon Kanawa) saboda yadda take jagoranci wajen tabbatar da cewa al’ummar Jihar Kano suna rabauta daga ribar dimokuradiyya da Kuma tallafawa al’umma ba tare da nuna gajiyawa ba.

Hakan ce ta sanya Goggon Kanawa ta kasance Uwa tagari duba da wancan kokari da take yi wajen halartar dukkanin guraren da ake hidimar taimakon mutane maza da mata ba tare da nuna kasala ba, sannan ko shakka babu mai girma Uwar-gidan Gwamnan Jihar Kano ta sami martaba da daraja dangane da wannan kokari da ta ke yi kan hidimar taimakon al’umma a fadin Jihar Kano.

Duk da cewa lokaci ba zai bari a fayyace dukkanin irin dawainiyar da mai dakin mai girma Gwamnan Kano ke yi ba, amma dai zan iya dan gutsura wasu daga cikin abubuwan da ta ke yi da wadanda ta ke sawa ake gabatar wa domin tabbatar da cewa rayuwr al’umma tana ci gaba da tafiya cikin yanayi mai kyau, musamman a wannan lokaci na kalubalen rayuwa da ake ciki.

A matsayina na mai bibiyar abubuwan da Uwar-gidan Gwamnan ke yi tun lokaci mai tsawo, ina mai kara jaddada cewa al’ummar Jihar Kano suna yi mata kallo guda biyu. Na farko ana yi mata kallon shugaba mai kokarin assasa aiyukan alheri domin ci gaban al’umma. Sannan ana yi mata kallon matsayin Uwa mai dora shugabanni bisa sahihiyar hanya musamman ga al’ummomin da suka zabe su a tsarin dimokuradiyya.

Idan aka dauki dalili na farko, za a yarda da ni cewa Farfesa Hafsat Abdullahi Umar Ganduje uwa ce wadda tun dadewa ta ke dora shugabanni zababbu ko nadaddu a Gwamnatin Jihar Kano kan hanyar yin abubuwa na kyautatawa al’ummomin su wadanda suka zabesu kan madafun iko daban-daban. Sannan dalili na biyu tana kokari Kwarai da gaske wajen halartar ire-iren wadancan tarurruka na bada tallafi ga mutane wanda Kuma zuwan ta yana Kara bunkasa tallafawa al’umma daga masu mulki daga matakai daban-daban.

Bugu da kari, a matsayina na wanda yake halartar kusan dukkanin inda mai girma Uwar-gidan Gwamnan Jihar Kano ke zuwa domin halartar aikin tallafawa al’umma, ina jaddada cewa idan har masu rike da madafun iko zasu ci gaba da tafiya a doron bada tallafi ga al’umma ko shakka babu za a sami zaman lafiya da zamantakewa mai albarka sannan kuma hakan zai sanya a lokutan zabe a sami nasarori saboda waccan dangantaka ta bada tallafi ga al’umma wadanda sune masu zabe.

A wannan gabar nake kara jaddada cewa Uwar-gidan Gwamnan Jihar Kano Farfesa Hafsat Abdullahi Umar Ganduje ta ciri tuta tare da kasancewa jagorar taimakon al’umma da kuma kawo managarcin sauyi a siyasa da zamantakewa da kuma samar da yanayi mai tsari wajen jituwa tsakanin masu rike da madafun iko da talakawan su.

Kafin in kammala wannan makala tawa, zan yi amfani da wannan dama wajen jinjinawa mai girma Uwar-gidan Gwamnan Jihar Kano saboda kokarin da ta ke yi wajen ganin ana kyautata wa al’umma a kodayushe wanda hakan ta jawo wa Jihar kano ci gaba da bunkasar tattalin arziki da Kuma fahimtar juna tsakanin talakawa da masu mulki.

Sannan Ina fata cewa mai girma Farfesa Hafsat Abdullahi Umar Ganduje za ta ci gaba da hakuri da dukkanin wani kalubale daga wadanda suke ganin watakila abubuwan da ake yi basu yi masu dadi musamman kan yadda ake ta kokarin ganin kowa yana amfana da romon dimokuradiyya a kowane lungu da sako na fadin Jihar Kano.

Jabiru ya rubuto wannan makala daga Dungurawa Karamar hukumar Dawakin Tofa, Jihar Kano. (jabiru.hassan@yahoo.com)

Leave a Reply