Babban bankin Najeriya (CBN) ya sanar da sabbin dokokin hada-hadar Naira wadanda zasu fara aiki a farkon shekarar 2023 a ranar tara ga watan Janairun shekarar (9/01/2023).
Neptune Prime Hausa ta kawo maku abubuwan da ya kamata ku sani game da haka;
1-Duk wanda zai cire kuɗi a asusun ATM, Naira dubu ashirin kawai zai iya cirewa a rana ɗaya,haka kuma, Naira dubu ashirin kawai mutum zai iya cirewa a rana a asusun POS.
2- A mako guda Naira dubu ɗari kacal mutum zai iya cirewa a ATM ko a POS
3-Takardun Naira 200 sune mafi girman takardun kuɗi da za a dinga sanyawa a ATM
4- Mafi yawan kuɗin da mutum zai iya fitarwa a cikin banki a wuni shine Naira dubu ɗari (₦100,000), Ma’aikata kuma mafi yawan kuɗin da za ta iya cira shine Naira dubu ɗari biyar.
KU KUMA KARANTA:Shugaba Buhari ya kaddamar da sabbin takardun kuɗi
Idan da akwai dalilin da zai sanya mutum ko masana’anta ta cire kuɗin da ya haura adadin da aka ƙayyade za a biya kuɗin kwamasho, idan mutum ne zai cire sama da adadin ba kamfani ko ma’aikata ba, zai biya kudin kwamasho na kashi biyar cikin dari da adadin kudin da zai cire wato 5%.
Idan kuma kamfani ne ko ma’aikata, zasu biya kudin kamisho na kashi goma cikin ɗari wato 10% na abinda zai cire.
- Dukkanin kuɗin da za’a cire ta hanyar wani ya baka Cheque wato 3rd Party Cheque na kudin da ya haura naira dubu hamsin (₦50,000) dole sai a kanta za a cire.