Gwamnan Zamfara Ya Fi Kowa Kishin Jihar – Dokta Shinkafi

0
387

Daga; IMRANA ABDULLAHI.

AN bayyana Gwamnan Jihar Zamfara Dokta Muhammad Bello Matawalle, a matsayin wanda ya fi kowa kishin Jihar Zamfara tare da al’ummarta baki daya.

Dokta Suleiman Shu’aibu Shinkafi, mai ba Gwamnan shawara a kan harkokin hulda da kasashen waje ne ya bayyana hakan lokacin da yake mayar da martani ga masu sukar Gwamnan a game da batun yan yi wa kasa hidima da za su samu horo a wani sansani cikin Jihar Katsina.

“Ai kamar yadda kowa ya Sani babu wani mutum da ya kai Gwamnan Jihar Zamfara kishi da ganin martaba da mutunta al’ummar Jihar kamar Gwamna Muhammad Bello Matawalle, domin ya kan kwashe tsawon watanni uku ba tare da ya fita daga cikin Jihar ba, ya na gudanar da aikin ci gaban Jihar ne Dare da rana domin samun walwala da jin dadin jama’a”.

Dokta Shinkafi ya ci gaba da cewa ya na da kyau ga duk wanda zai yi wata magana ya tsaya domin gudanar da bincike, kasancewar Gwamna Bello Matawalle mutum ne mai kokarin ganin bayan duk wata matsalar da Jihar take fuskanta.

“Duk da ba wai wani abu ne ke shigowa Jihar ba sai kudin daunin da ake samu na wata- wata da ake bayar wa daga Gwamnatin tarayya, amma duk da hakan Gwamna Muhammad Bello Matawalle baya yin kasa a Gwiwa wajen ciyar da Jihar gaba”.

Don haka muke kokarin fadakar da jama’ar da ba su san me Jihar Zamfara ke ciki ba da su hanzarta zuwa cikin Jihar domin tantance gaskiyar lamarin.

“Mu ba zamu amince da duk wani nau’in cin fuska ba ga Gwamna ko Gwamnatin Jihar Zamfara ba, don haka muke yin kira ga duk wani ko wasu da ke ganin za su bari ayi amfani da su cewa su hanzarta barin hakan domin ba zamu amince da hakan ba”, inji Dokta Suleiman Shu’aibu Shinkafi.

Ya kara da cewa ba a taba samun Gwamna kamar Muhammad Bello Matawalle ba da ke kokarin ganin martaba da mutuncin Jihar Zamfara ya kara daukaka a tsakanin idanun duniya ba, wanda hakan ya Sanya Gwamnan ke kokarin lalubo hanyoyi a tsakanin kasashen waje da za su amfani Jiha da al’ummarta a dukkan fannoni na rayuwa.

Dokta Shinkafi, ya kuma bayar da tabbacin cewa “ba zamu zura idanu haka kawai mu rika ganin wadansu masu son zuciya na kokarin yin yarfen siyasa ga Gwamna ko Gwamnatin Jihar Zamfara ba, saboda mu shaidu ne a kan irin Namijin kokarin da Gwamnan ke yi domin kawo ci gaban da kowa zai amfana a Jihar da kasa baki daya”.

“Kowa ya Sani duk wanda ya ce kule zamu ce masa Cas don ba gudu ba ja da baya ko kadan”.

Leave a Reply