SHEKARU 80: Al’umma Sun Yaba Da Irin Sadaukarwar Alhaji Bawa Garba (ABG)

0
542

Daga; USMAN NASIDI, Kaduna.

A RANAR 18 ga watan Fabrairu na shekarar 2022 Dattijo Alhaji Bawa Garba wanda aka fi sani da suna (ABG) ke cika shekaru 80 da haihuwa a duniya.

Wadannan shekaru na wannan Dattijo sun zama abin ci gaba da alfahari a gare shi duba da yadda ya sadaukar da rayuwar shi wajen gudanar da taimakon Jama’a ta fuskoki da dama ba tare da tsunduma kan shi cikin harkokin siyasa ba.

Sunan (ABG) ya yi tambari a kasar nan a matsayin wani tauraro mai haskawa wanda ya zama baya mai goya marayu wajen taimako da inganta rayuwar marasa ƙarfi.

Ga dukkanin wanda ya san (ABG) a tsawon shekarun da ya shafe yana ayyuka babu, shakka zai yi zaton Dattijon a yanzu ya haura wadannan shekaru na 80, wanda hakan ke nuna cewa wannan bawan Allah ya fara ayyukan taimakon al’umma tun yana matashi ɗan shekaru 20.

Tarihi ya nuna yadda Alhaji Bawa Garba (ABG) ya samar da makaranta ta yaƙi da jahilci ga jama’ar Arewa tun a shekarun 1967 zamanin yaƙin basasa inda ya ilmantar da ɗaruruwan jama’ar Arewa a wani yunkuri na kishin yankin da ganin an cike gurbin da ke da shi a tsakanin bangaren Kudu da Arewa.

A fili yake, Alhaji Bawa Garba (ABG) mutum ne mai fikira wanda ya tsara rayuwar shi wajen bunƙasa harkokin kasuwanci dake tafiya da zamani a Najeriya musamman a yankin arewacin kasar.

An haifi Alhaji Bawa Garba (ABG) a garin Garkiɗa dake yankin ƙaramar hukumar Gombi ta Jihar Adamawa, kuma ya fara nuna kwazo akan ayyukansa tun yana yaro karami a harkar noma da kiwo tare da mahaifinsa.

Bai yi ƙasa a gwiwa ba wajen shiga harkokin kasuwanci inda ya yi suna sosai a babbar kasuwar baje koli ta duniya wadda ta fara ci a shekarar 1979 a Kaduna.

Dattijo Alhaji Bawa Garba (ABG) ya kasance sahun farko na wadanda suka fara harkar samar da tauraron Ɗan Adam a Najeriya inda ya samar da Kamfanin tauraron Ɗan Adam a biranen Kaduna da Legas tare da ɗaukar dubban matasa aiki.

Tarihin cigaban birnin tarayya Abuja ba zai cika ba sai sai an ambato irin kwazo da Alhaji Bawa Garba ya yi musamman a shekarar 2006 lokacin da Nasiru El-Rufa’i yake matsayin Ministan Abuja, ta fuskar sufuri inda ya samar da motocin ɗaukar fasinja sama da 150 dake Jigilar babban birnin.

Akwai rayuwa abin koyi dangane da halayyar Dattijo Alhaji Bawa Garba (ABG) duba da irin kyakkyawar rayuwa da ya yi wajen taimakon jama’a, Hakazalika ɓangaren iyalinsa ya ba da kyakkyawar kulawa a gare su lamarin da a yau dukkanin ‘ya’yansa ke cikin rayuwa ingantacciya abin so ga kowa da kowa.

Matukar ana magana akan dattawa da Dattaku ya zama wajibi a sanya Alhaji Bawa Garba (ABG) a ciki matsayin abin koyi wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen ganin rayuwar al’umma ta cigaban matasa sun zama abin alfahari ga Jama’a.

Muna amfani da wannan dama wajen taya iyalan Alhaji Bawa Garba (ABG) murna da wadannan shekaru masu daraja da albarka, muna taya ‘yan uwa da iyalan Alhaji Bawa Garba ABG murna da wannan baiwa da Allah ya basu Allah ya karo masa wasu shekaru masu albarka da ƙarin lafiya Allahumma Amin.

Leave a Reply