Shaguna 100 sun ƙone a gobarar kasuwar fanteka a Kaduna

0
100

Aƙalla shaguna 100 ne suka ƙone a wata gobarar da ta tashi a tsakar dare a kasuwar fanteka da ke garin Kaduna.

Gobarar ta tashi ne kafin wayewar garin Laraba a kasuwar fanteka da ke kusa da harabar Kwalejin Kimiyya da Kere-kere (Kaduna Polytechnic).

Kasuwar fanteka wanda ke kusa da gidan gwamnatin jihar Kaduna a unguwar Tudun Wada, ta yi fice wajen kasuwancin kayan gini da karafa dangoginsu da sauransu.

Sakataren ƙungiyar ’yan kasuwar Fanteka, Ibrahim Muhammad, ya ce gobarar ta fi yin ɓarna a bangaren masu sayar katako.

KU KUMA KARANTA: Gobara ta hallaka wani magidanci, matarsa da ‘ya’yansa biyar a Kano

Ibrahim Muhammad ya ce, “masu gadin kasuwar sun shaida mana cewa ’yan mintoci kaɗan bayan karfe 12 na dare wutar ta fara ci daga ɓangaren ’yan katako.

“Sai da jami’an hukumar kashe gobara suka zo daga Jaji aka kashe gobarar da misalin kare 5 na asuba.

“Shagunanmu sama da 100 sun ƙone, amma yanzu dai ba za mu iya faɗan girman asarar da dukiyar aka yi ba,” in ji shi.

Sakataren ƙungiyar ’yan kasuwar ya ƙara da cewa ba a kai ga gano musabbabin tashin gobarar ba.

Leave a Reply