Gobara ta hallaka wani magidanci, matarsa da ‘ya’yansa biyar a Kano

0
87

Wani magidanci mai suna Shu’aibu Ahmad mazaunin unguwar Tudun Wada Brigate a ƙaramar hukumar Nassarawa a birnin Kano, ya rasa ransa tare da matarsa Binta da ‘ya’yansu guda 5.

Hakan ya faru ne sakamakon tashin wata mummunar gobara da ta afku dalilin kawo wutar lantarki mai ƙarfin gaske da misalin ƙarfe 12 na daren Lahadin da ta Gabata.

Muneer Ibn Ibrahim shi ne mai gidan hayar da suke, ya sheda cewa, wani firinji ne yai sanadin tashin gobarar bayan ya kama da wuta a lokacin da aka kawo wutar, shi kuma marigayin da iyalansa suna bacci ɗakin nasu kuma a rufe.

KU KUMA KARANTA: Gobara ta cinye ɗaruruwan shaguna a kasuwar Gwarzo

Wannan dalilin ya jawo hayaƙi ya turniƙe su inda hakan yai sanadiyar mutuwarsu su bakwai lokaci ɗaya.

An yi jana’izarsu kamar ya addini ya tanadar.

Allah ya jikansu da rahama Allah ya kyautata makwancinsu.

Leave a Reply