PDP ta lashi takobin hukunta Wike kan yi mata zagon ƙasa

0
185

Jam’iyyar PDP ta sha alwashin hukunta tsohon gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike da wasu ’ya’yanta kan yi mata zagon ƙasa a zaɓen 2023.

Da yake amsa tambayoyin manema labarai a ranar Talata, muƙaddashin shugaban jam’iyyar na ƙasa, Ambasada Umar Damagum ya bayyana cewa baya ga Nyesom Wike, akwai wasu ’ya’yan jam’iyyar da suka yi mata maƙarƙashiya a lokacin zaɓen da ya gabata.

Ya yi nuni da cewa, shugabancin jam’iyyar ya kafa kwamitin da duba abin da ya faru da kuma dalilan faɗuwar jam’iyyar a zaɓukan 2023.

Ya ƙara da cewa PDP za ta ɗauki matakan da suka dace idan aka gabatar da rahoton ga kwamitin gudanarwa na ƙasa (NWC).

Damagum ya kuma nace cewa babu wanda ke sama da jam’iyyar, “idan Wike yana tunanin cewa yana sama da wannan jam’iyyar, za mu iya nuna masa iya gudun ruwansa.”

KU KUMA KARANTA: Ƴan majalisar dokokin Ribas 27 sun fice daga PDP

Ya ce: “A ko yaushe ina fadar cewar muddin kai dan jam’iyyar PDP ne, dole ne ka yi mata biyayya.

“Aikina shi ne na daidaita wannan jam’iyya ba haifar da rikici ba.

“Kuma zan ci gaba da yin hakan sannu a hankali.

“Kuma, ba Wike kaɗai ba ne, akwai wasu mutanen da suka yi adawa da wannan jam’iyyar; idan muka kammala bincike za mu hukunta kowa.

“A halin yanzu, mun kafa kwamitin da zai yi bitar abubuwan da suka faru a 2023.

“Za su kawo mana rahoton abin da ya faru kuma duk wanda muka samu da laifi tabbas zai fuskanci hukunci,” in ji shi.

A makon jiya sakataren yaɗa labaran PDP na kasa, Debo Ologunagba ya ce shugabannin jam’iyyar na son mayar da hankali kan yin sulhu a tsakanin ‘ya’yan jam’iyyar da aka bata wa rai a baya maimakon saka kafar wando ɗaya da su.

Leave a Reply