Ƴan majalisar dokokin Ribas 27 sun fice daga PDP

0
145

Siyasa a jihar Ribas ta ɗauki sabon salo inda 27 daga cikin ’yan majalisar dokokin jihar 32 suka sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa APC.

Enemi George, ya tabbatar da hakan ga manema labarai cewa ’yan majalisar 27 na ƙarƙashin jagorancin Martin Amaewhule.

Ya ce sun ɗauki matakin ne a zaman da suka yi da safiyar ranar Litinin.

An shafe makonni ana takun saka tsakanin Amaewhule da wani ɗan majalisa mai suna Edison Ehie kan rikicin shugabancin majalisar.

Ana kyautata zaton Amaewhule na yin biyayya ga tsohon gwamna Nyesom Wike yayin da shi kuma Ehie yake na hannun dama Gwamna Siminalayi Fubara ne.

Majalisar a ƙarƙashin Amaewhule a watan Oktoba ta gabatar da sanarwar tsige gwamnan tare da tsige Ehie a matsayin shugaban majalisar.

KU KUMA KARANTA: Tinubu ya sa baki don daidaita rikicin siyasar Ondo

Sai dai nan take wasu ’yan majalisar masu biyayya ga Fubara suka tsige Amaewhule tare da naɗa Ehie a matsayin sabon shugaban majalisar.

Rikicin da ya ɓarke a majalisar mai mambobi 32 ya samo asali ne daga rashin jituwar Fubara da uban gidansa, Wike, wanda yanzu shi ne Ministan Babban Birnin Tarayya.

Duk da cewa ’yan siyasar biyu sun halarci taro makonnin da suka gabata kuma ga dukkan alamu an samu sasanci.

Amma da ficewar ’yan majalisar 27 daga PDP zuwa APC a ranar Litinin ya buɗe sabon babi a siyasar jihar.

A halin da ake ciki kuma, a ƙarshen mako ne wasu ’yan siyasa daga jam’iyyun SDP da APC suka sauya sheka zuwa PDP.

Masu sauya shekar su ne mataimakiyar ’yar takarar gwamna a SDP a zaɓen 2023, Patricia Ogbonnaya; da tsohon Shugaban Ahoada ta Yamma, Karibo Wilson.

Sun sauya sheka ne tare da magoya bayansu da sauran jiga-jigan jam’iyyar.

’Yan siyasar sun sauya shekar ne don yin biyayya ga Fubara.

Leave a Reply