Menene manhajar ‘Kapo drive’?

0
216

Wanda ya ƙirƙira manhajar ‘Kapo drive’ ya ziyarci ofishin jaridar Neptune Prime dake Abuja, inda ya gana da shugaban Neptune Prime, Dr. Hassan Gimba.

Neptune Hausa ta tattauna da ya ƙirƙiro manhajar ‘Kapo drive’, ga yadda tattaunawan ta kasance:

Neptune Hausa – Tarihin rayuwar ka

Muktar – Sunana Muktar Auwal, an haife ni a jihar Yobe, shekaruna 26. Nayi firamare da sakandare a garin Abuja da jihar Kano, nayi jami’ar El-Razi dake ƙasar Sudan, na karanci Ilimin Kasuwanci da Ilimin Lissafin Kuɗi.

Neptune Hausa – Menene manhajar Kapo drive?

Muktar – Manhaja ce da za ta sauƙaƙa tafiye-tafiye, da kuma farashi mai rahusa. Kuma muna so mu ga mun zarce sauran manhajar tafiye-tafiye, wanda ba na ƙasan nan bane, suna kuma chaji kashi 25 cikin 100, wannan ‘Kapo drive’ in na ɗan ƙasa ne kuma muna chaji kashi 10 cikin 100. Za mu rage matasa masu zaman banza, da samar musu da abin yi.

Neptune Hausa – Manhajar a duk Najeriya ce ta ke aiki?

Muktar – A yanzu a jihohi biyu ne, garin Abuja da jihar Kano. Amma muna sa ran a wasu jihohin nan ba da jimawa ba.

Neptune Hausa – Yanzu kamar motoci nawa kuke da su?

Muktar – Muna da motoci ɗari a yanzu, hamsin a garin Abuja, hamsin a jihar Kano. Amma muna sa ran ƙara motoci cikin wata uku da fara aiki. Kuma App ɗinmu ‘bridge’ ne wanda zai yi haɗa fasinjoji da direbobi. Wajen rajista akwai na fasinjoji da kuma na direbobi.

Neptune Hausa – Me ya jawo ra’ayin ka akan manhajar?

Muktar – Rashin abin yi ga matasa ne ya janyo ra’ayi na, da kuma rashin ilimin kimiyya da fasaha a jihohin arewa. Ina sa ran cire dubban mutane daga cikin wannan matsalar. Wannan manhajar zai samar da aikin yi ga mutum sama da dubu goma cikin wata uku.

KU KUMA KARANTA: Manhajar ‘Threads’ da yadda ake amfani da ita

Neptune Hausa – Yaushe za a fara anfani da manhajar?

Muktar – Za mu fara amfani da shi a garin Abuja a ranar 15 Disamba, 2023.
A jihar Kano kuma ranar 17 Disamba, 2023 da yardar Allah. Daga wannan ranar zaka sami manhajar a Play store, Apple store, IOS.

Muktar Auwal

Neptune Hausa – Kana da masu ɗaukan nauyin wannan manhajar ne?

Muktar – Ni kaɗai ne, bani da wanda ke ɗaukan nauyin. Amma ina so in akwai masu ɗaukan nauyin, ina maraba da su.

Neptune Hausa – Me burin ka?

Muktar – Ina son na faɗaɗa wannan manhajar ta isa duk jihohin arewacin Najeriya. Da kuma buɗe iyakoki a duk jihohin.

Neptune Hausa – Akwai abubuwan da za mu tsammani nan gaba?

Muktar – Ƙwarai kuwa, ina sa ran ƙara motoci wanda zai dinga tafiye-tafiye daga gari zuwa gari. Da kawo bas na ɗaukan mutane dayawa.

Neptune Hausa – Daga ƙarshe me za ka ce?

Muktar – Ina godiya ga Allah da ya bani damar buɗe wannan manhajar, ina kuma kira ga matasa musamman ƴan arewa da kada su karaya a burikan su.

Neptune Hausa – Mungode da bamu lokacin ka.

Muktar – Ni ma nagode.

Leave a Reply